Jagoran Jam'iyyar APC Bola Tinubu Zai Jagoranci Lakca a Cibiyar Arewa karo na 11

Jagoran Jam'iyyar APC Bola Tinubu Zai Jagoranci Lakca a Cibiyar Arewa karo na 11

- Jagoran APC kuma tsohon gwamnan jihar Lagos, Bola Ahmed Tinubu zai jagoranci gudanar da lakcar cibiyar Arewa wato 'Arewa House' da aka saba yi duk shekara.

- Daractan Arewa House, Dr Shuaib Aliyu ne ya sanar da haka ga manema labarai a Kaduna

- Haka zalika an bayyana gwamnan jihar Plateu, Lalong a matsayin wanda zai gudanar da Lakca a wajen taron.

Jagoran jam'iyyar APC na kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai shugabanci lakcar da za'a gudanar a cibiyar Arewa karo na 11 a ranar Asabar.

Daraktan wurin, Dr Shuaibu Shehu Aliyu ya fada ma yan jarida a Kaduna ranar Alhamis, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Tinubu ya tsallake mutanen da gobara ta shafa a Legas da Oyo, amma ya baiwa na Katsina N50m: Omokri

Yace lakcar karshe wato ta 10, wadda gwamnan babban bankin Najeriya na wancan lokacin, Sanusi Lamido Sanusi, ya gabatar kuma Oba na Lagos Oba Rilwan Akiolu ya shugabanta.

A yanda yace, An lura sosai wajen zabar Tinubu da Lalong domin jagorantar lakcar.

Jagoran Jam'iyyar APC Bola Tinubu Zai Jagoranci Lakca a Cibiyar Arewa karo na 11
Jagoran Jam'iyyar APC Bola Tinubu Zai Jagoranci Lakca a Cibiyar Arewa karo na 11 Hoto: @AsiwajuTinibu
Asali: Twitter

A cewarsa:

"Ina mai farin cikin sanar daku cewa gwamnan jihar Filato Simon Bako Lalong zai gudanar da lakcar wannan shekarar a karkashin jagorancin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a ranar 27 ga watan Maris na 2021."

Lakcar wacce aka shirya ta musamman domin wayar da kai kan hadin kan kasa.

An zabi gwamna Lalong ne duba da cewa shine shugaban gwamnonin Arewa da kuma kwarewar sa wajen jagorantar jihar Filato.

Ana ma gwamnan kallon ya zayyi da rikice-rikicen jihar na tsawon shekaru 20 baya. Amma daga hawan sa mulki ya samu ya kawo karshen wadannan rikice-rikicen.

KARANTA ANAN: Rashin aikin yi cikin matasan Karkara ke rura wutan matsalar tsaro, Buhari

"Haka kuma dangane da shugabanci, a koda yaushe muna duba ayyukan da muhimman mutane sukayi kafin mu zabi wanda zai shugabanci lakcar. Asiwaju Bola Tinubu an zabe shi domin ya kara ma taron armashi da kuma kawo cigaba da hadin kan kasa" inji Daraktan.

Ya bayyana cewa lakcar shekara-shekara ta cibiyar Arewa wato 'Arewa House' ta kasance ana gudanar da ita tun shekarar 1994.

Kuma lakcar ta kunshi kowa da kowa ba tare da duba da kabila, addini ko kuma siyasa ba.

A na dai gabatar da lakcar ne domin girmama tsohon Firimiyan Arewacin Najeriya, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto.

Gwamna Lalong zai yi magana ne akan 'yadda za'a rage yawan kashe kuɗi a gwamnati da kuma sanya matasa wajen kawo cigaban kasa bayan annobar Korona.

A wani labarin kuma Na gano ‘Yan bindigan da su ka sace Dalibai 38 a Kaduna, a ban damar zama da su inji Gumi

Shahararren malamin addinin musulunci, Ahmad Abubakar Gumi, ya yi magana game da wasu daliban makarantun gandu ta Kaduna da aka yi garkuwa da su.

Shehin ya ce umarnin da aka ba jami’an ya hana a iya zama da ‘yan bindiga.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban- daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77 .

Asali: Legit.ng

Online view pixel