Yanzu Yanzu: Limaman Harami sun hadu domin tsara Jadawalin sallolin Taraweeh da Tahajjud na watan Ramadana

Yanzu Yanzu: Limaman Harami sun hadu domin tsara Jadawalin sallolin Taraweeh da Tahajjud na watan Ramadana

- Hukumomin kasar Saudiyya sun fitar da jerin sunayen manyan limaman da za su jagoranci bayar da sallolin Tarawi da Tuhajjud a masallacin Harami

- Limamai shida ne za su jagoranci bayar da sallolin a Azumin Ramadana na bana

- A yanzu haka Limaman sun hadu don fitar da jadawalin yadda lamarin zai kasance

Rahotanni sun nuna cewa manyan Limaman Harami sun hadu domin tsara Jadawalin sallolin Taraweeh da Tahajjud na watan Ramadana.

Tuni dai hukumomin kasar ta Saudiyya suka fitar da jerin sunayen manyan limaman da za su jagoranci bayar da sallolin Tarawi da Tuhajjud a masallacin Harami da ke kasa mai tsarki a azumin wannan shekarar ta 2021.

Hakan na kunshe ne a cikin wata wallafa da shafin Twitter na Haramain Sharifain ya yi a ranar Laraba, 24 ga watan Maris.

KU KARANTA KUMA: Dalla-dalla: Hanyoyin da za ka bi don yin rijistar jarabawar UTME na 2021

Yanzu Yanzu: Limaman Harami sun hadu domin tsara Jadawalin sallolin Taraweeh da Tahajjud na watan Ramadana
Yanzu Yanzu: Limaman Harami sun hadu domin tsara Jadawalin sallolin Taraweeh da Tahajjud na watan Ramadana Hoto: @hsharifain
Asali: Twitter

Wallafar ya kuma bayyana cewa limamai shida ne za su jagoranci gudanar da sallolin a azumin bana.

Musulmi a duniya na sanya ran fara Azumin Ramadana na wannan shekarar a cikin watan Afirilu mai kamawa.

Har ila yau, hukumomin Saudiyya sun ce bana babu wasu Limamai da za a gayyato domin limancin sallolin, kamar yadda ake gani a shekarun da suka gabata.

KU KARANTA KUMA: 2023: Wani Matashi ɗan Shekara 35 daga Arewacin Najeria zai tsaya takarar shugaban ƙasa a APC

Ga cikakkun sunayen limaman da za su ja ragamar sallolin Tarawi da Tuhajjud.

1. Sheikh Abdul Rehman Al Sudais

2. Sheikh Saud Al Shuraim

3. Sheikh Abdullah Awad Al Juhany

4. Sheikh Maher Al Muaiqly

5. Sheikh Bandar Baleelah

6. Sheikh Yasir Al Dossary

A gefe guda, a makon da ya gabata ne aka yi ta watsa wani bidiyo da ke nuna yadda sararin samaniyar Masallacin Ka'aba da ke kasar Saudiyya ya rikide ya zama ja jazur.

Da yawan mutane sun yi ta yada bidiyon tare da nuna yadda lamarin ya kasance, suna nuna hakan a matsayin wata alama mai nuna cewa duniya tazo karhse.

A sakon da ke yawo tare da bidiyon an ce: ... "wannan ne abin da ya faru a Saudiyya a yau, iska mai tafe da guguwar rairayin hamada mai launin ja ta rufe sararin samaniyar Masallacin Harami da kewaye."

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng