Ka nemi sulhu da 'yan bindigar nan tun kafin su kashe 'ya'yan mu, Iyayen Ɗalibai ga El-Rufa'i

Ka nemi sulhu da 'yan bindigar nan tun kafin su kashe 'ya'yan mu, Iyayen Ɗalibai ga El-Rufa'i

-Iyayen ɗaliban da aka sace a makarantar koyon zamanantar da gandun daji FCFM sun roƙi gwamnan Kaduna da ya fara tattaunawar sulhu da yan bindigan

- Ɗaya daga cikin iyayen kuma ma'aikaci a makarantar ya bayyana haka, kuma yace su tsoron su kada a kashe 'yayan su

- Ya kuma ce ya kamata gwamnan Kaduna Malam Nasiru Elrufa'i ya jingine kudirinsa na 'Babu biyan kuɗin fansa' don tattaunawa da yan bindigan.

Iyayen ɗalibai 39 da aka sace a kwalejin zamanantar da gandun daji (FCFM) sun yi kira ga gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Elrufa'i ya tattauna da yan bindigar da suka sace yayan su don ganin an sako su.

KARANATA ANAN: 2023: Wani Matashi ɗan Shekara 35 daga Arewacin Najeria zai tsaya takarar shugaban ƙasa a APC

Iyayen sun nuna matuƙar damuwa da cewa yan biindiga sun sace 'yayan su tsawon sati biyu kenan a ɗakunan kwanan su, amma har yanzun basu sako su ba.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa a kwanakin baya, yan bindiga sun farmaki makarantar FCFM kuma suka yi awon gaba da ɗalibai mata 23 da maza 16.

Daga baya 'yan bindigar sun saki wani faifan bidiyo na halin da ɗaliban ke ciki kuma suka buƙaci a biyasu 500 miliyan kuɗin fansa.

Bayan haka, jami'an tsaro sun bayyana cewa sun kuɓutar da ɗalibai 180 amma 39 na hannun 'yan bindigar.

Ya yin da yake jawabi ranar Alhamis, ɗaya daga cikin ma'aikatan makarantar kuma wakilin iyayen da abun ya shafa, Sani Friday, ya ce iyayen na tsoron kada yan bindigan su kashe ɗaliban idan gwamnati ta nuna zatai amfani da ƙarfi.

Sani Friday, wanda 'ya'yansa biyu na cikin waɗan da aka tafi da su, ya roƙi gwamna Elrufa'i ya janye kudirinsa na 'babu biyan kuɗin fansa' don tattaunawa da su kan sakin ɗaliban.

Ka nemi sulhu da 'yan bindigar nan tun kafin su kashe 'ya'yan mu, Iyayen Ɗalibai ga El-Rufa'i
Ka nemi sulhu da 'yan bindigar nan tun kafin su kashe 'ya'yan mu, Iyayen Ɗalibai ga El-Rufa'i Hoto: @elrufai
Asali: Twitter

Sani yace: "Wannan gwamnan ne a baya yace idan har zai biya 'yan bindiga kuɗi su daina kashe masa yan jiharsa, to a shirye yake ya biya su ko nawa ne."

"Amma yanzun gwamnatin jihar nan ta fito ta bayyana cewa, ba dai-dai bane tattaunawa da yan bindiga kuma bazata tattauna dasu ba, sun bayyana haka tun kafin a sace yayan mu."

KARANTA ANAN: Sojoji sun sheke 'yan bindiga 2 yayin da suka kai samame maboyarsu a Kaduna

"Bayan wancan jawabin sai kuma wannan lamarin ya faru. Kuma har yanzun gwamnatin na kan bakarta na bazata tattauna da yan bindiga ba."

Sani Friday ya ƙara da cewa: "Amma tun kafin wannan Elrufa'i ya bayyana cewa zai iya yin komai ga 'yan bindiga don su dai na kashe-kashen da suke yi. To yanzun muna son ya yi wani abu,"

"Tsoron da mukeji shine gwamnati na ganin zata iya amfani ɗa karfinta ta ƙwato ɗaliban. Wanda hakan babbar matsala ce saboda yan bindigan a ankare suke."

"Zasu iya kashe ɗaliban gaba ɗayan su idan suka gano gwamnati na ƙoƙarin yin amfani da ƙarfi a kansu sabida ƴaƴan mu sune garkuwar su."

"Mu abinda mukeso gwamnati ta fara yi shine tattaunawar sulhu dasu, koda zata yi amfani da karfin to ya biyo bayan tattaunawar," a cewar Sani Friday.

A labarin kuma JAMB ta bayyana Ranar da zata fara saida Fom ɗin Zana Jarabawar UTME 2021

JAMB ta sake jaddada cewa duk wani dalibi da ke son zana jarabawar to ya zama wajibi ya mallaki lambar katin zama dan kasa wato NIN.

Ta Bayyana za'a fara siyar da fom din ranar takwas ga watan Aprilun wannan shekarar da muke ciki.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77.

Asali: Legit.ng

Online view pixel