'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari A Kaduna, Sun Kashe Huɗu Sun Raunata Wasu

'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari A Kaduna, Sun Kashe Huɗu Sun Raunata Wasu

- 'Yan bindiga sun sake kai hari kananan hukumomin Igabi da Jema'a a jihar Kaduna

- Maharan sun halaka mutane uku a Kauyen Ungwan Lalle sun kuma kashe guda a Golgofa

- Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya bada sanarwar

Wasu yan bindiga sun kai hari a kananan hukumomin Igabi da Jema'a a Jihar Kaduna, inda suka kashe mutane hudu suka raunata wasu da dama, The Punch ta rwuaito.

A cewar kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Mr Samuel Aruwam, cikin sanarwar da ya fitar ya ce an kashe mutane uku a kauyen Ungwan Lalle da ke karamar hukumar Igabi.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Ba Za Su Ajiye Makamai Ba Sai An Basu Tabbacin Babu Abin Da Zai Same Su, Sheikh Gumi

'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari A Kaduna, Sun Kashe Hudu Sun Raunta Wasu
'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari A Kaduna, Sun Kashe Hudu Sun Raunta Wasu. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

Ya ce an kai harin ne a safiyar ranar Litinin.

Ya ce sunayen wadanda aka kashe sun da da Dayyab Yarima, Dalhatu Ashiru da Suleiman Salamatu.

Kwamishinan ya kara da cewa dakarun sojoji na Operation Safe Haven sun bada rahoton cewa yan bindiga sun kai hari Niima Clinic da ke kauyen Golgofa a karamar hukumar Jema'a a ranar Litinin kuma sun kashe ma'ikaci a asibitin.

KU KARANTA: Angon Da Ya Auri Matar Da Aka Saka Wa Rana Da Ƙaninsa, Soja, Da Ya Mutu Ya Magantu

Ya ce gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai ya yi bakin cikin samun labarin ya kuma yi addu'ar Allah ya jikan wadanda suka riga mu gidan gaskiya.

Ya kuma yi wa wadanda suka samu rauni fatar samun sauki cikin gaggawa.

A wani labarin daban, hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, a ranar Litinin ta kama fitaccen mai wakokin yabon Annabi Muhammadu SAW, Bashir Dandago.

An kama shi ne kan zargin fitar da wakar da hukumar ta ce na iya tada fitina, da ta ce ya zagi malamai a jihar Kano kan matayarsu game da rikicin Sheikh AbdulJabbar Kabara.

Shugaban hukumar, Ismail Na'abba Afakallah ya tabbatarwa Daily Trust kamun.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel