Angon Da Ya Auri Matar Da Aka Saka Wa Rana Da Ƙaninsa, Soja, Da Ya Mutu Ya Magantu

Angon Da Ya Auri Matar Da Aka Saka Wa Rana Da Ƙaninsa, Soja, Da Ya Mutu Ya Magantu

- Sulaiman Mohammad, kanin sojan saman Nigeria, Abubakar Mohammad da ya rasu a Kaduna ya magantu kan auren matar da aka saka wa rana da kaninsa

- Sulaiman ya ce bayan rasuwar kaninsa iyalan matar, Hajara, sun aiko da sako cewa tana son shi don haka a maimakon janye auren kawai za ta aure shi a madadin yayansa

- Sulaiman ya ce yana da tsohuwar budurwa wacce ya yi wa bayanin abinda ya faru kuma ta amince ta ce babu damuwa

Sulaiman Mohammad, kanin Abubakar Mohammed, marigayin sojan saman Nigeria, NAF, ya yi bayanin abinda ya sa ya auri matar da aka saka wa rana da kaninsa, makonni biyar bayan rasuwar kanin.

Abubakar na cikin sojojin da suka kwanta dama sakamakon artabu da suka yi da yan bindiga a Ungwan Laya da ke kusa da Birnin Gwari a ranar 13 ga watan Fabrairu.

Angon Da Ya Auri Matar Da Aka Saka Wa Rana Da Ƙaninsa, Soja, Da Ya Mutu Ya Magantu
Angon Da Ya Auri Matar Da Aka Saka Wa Rana Da Ƙaninsa, Soja, Da Ya Mutu Ya Magantu. Hoto: @lindaikeji
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Irabor: Ƴan Boko Haram 500 Suna Gidan Yari, Wasu Za Su Shafe Shekaru 60 a Ɗaure

Ya rasu ana sati uku daurin aurensa da Hajara, wadda tuni ya wallafa hotunan kafin aurensu a dandalin sada zumunta.

Makonni kadan bayan rasuwar Abubakar, an daura wa Sulaiman da Hajara aure a ranar 20 ga watan Maris.

Mutane suna cigaba da bayyana mabanbanta ra'ayoyi game da aurensu.

Amma a hirar da BBC Pidgin, Sulaiman ya yi bayanin cewa Hajara ce ta nemi a daura musu aure bayan rasuwar yayansa.

DUBA WANNAN: Gwamnati Za Ta Iya Dena Biyan Tallafin Lantarki a Karshen 2021, In Ji Hadimin Buhari

"Abubakar yaya na ne kuma ina matukar sonsa kuma rasuwarsa ya min ciwo. Abin da ya faru shine bayan rasuwarsa, iyalan matar da zai aura suka aiko mana da sako," in ji shi.

"Sakon shine cewa ita (Hajara) tana so na kuma a maimakon a fasa auren wanda saura makonni uku a lokacin, zai fi dacewa in may gurbin yaya na in aure ta, gashi yanzu munyi aure."

Angon ya kuma yi bayanin cewa ya yi wa tsohuwar budurwarsa bayani a lokacin da abin ya faru kuma ta fahimta.

Sulaiman ya ce iyalan biyu duk sun amince da auren. Ya kara da cewa bai damu da abinda mutane ke fada ba a dandalin sada zumunta kan aurensa da Hajara.

A wani labarin daban, hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, a ranar Litinin ta kama fitaccen mai wakokin yabon Annabi Muhammadu SAW, Bashir Dandago.

An kama shi ne kan zargin fitar da wakar da hukumar ta ce na iya tada fitina, da ta ce ya zagi malamai a jihar Kano kan matayarsu game da rikicin Sheikh AbdulJabbar Kabara.

Shugaban hukumar, Ismail Na'abba Afakallah ya tabbatarwa Daily Trust kamun.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel