Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Ba Za Su Ajiye Makamai Ba Sai An Basu Tabbacin Babu Abin Da Zai Same Su, Sheikh Gumi

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Ba Za Su Ajiye Makamai Ba Sai An Basu Tabbacin Babu Abin Da Zai Same Su, Sheikh Gumi

- Sheikh Ahmad Gumi ya ce yan bindiga ba za su mika wuya ba sai sun tabbatar ba abinda zai same su

- Gumi ya kuma ce bai ga dalilin da zai sa gwamnati ta ki yin sulhu da yan bindigan da suka nuna sha'awar yin sulhun ba

- Babban malamin ya yi wannan jawabin ne yayin wani taron da aka yi kan kallaubalen tsaro da ke adabar Nigeria

Sheikh Ahmad Gumi, shahararren malamin addinin musulunci ya ce yan bindiga ba za su ajiye makamansu ba har sai an basu tabbacin babu abinda zai same su sannan za a taimaka musu.

Gumi ya yi wannan furucin ne a ranar Laraba yayin wani taro da aka yi ta yanar gizo da Cibiyar Nazarin Dokoki Da Demokradiyya ta shirya, The Cable ta ruwaito.

An shirya taron ne ne domin tattaunawa a kan kallubalen tsaro da ke adabar sassan Nigeria da dama.

DUBA WANNAN: Angon Da Ya Auri Matar Da Aka Saka Wa Rana Da Ƙaninsa, Soja, Da Ya Mutu Ya Magantu

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Ba Za Su Ajiye Makamai Ba Sai An Basu Tabbacin Babu Abin Da Zai Same Su, Sheikh Gumi
Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Ba Za Su Ajiye Makamai Ba Sai An Basu Tabbacin Babu Abin Da Zai Same Su, Sheikh Gumi. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

Malamin ya ce bai ga dalilin da zai sa gwamnati ba za ta yi sulhu da yan bindigan da suka amince suna son a yi sulhun ba.

Gumi ya ce, "Babu wanda zai iya hallasta laifi, abinda muka gani shine yakin kabilanci tsakanin wadanda ke daji da mutanen kauyen da ke makwabtaka da su. A lokacin da makiyayi ke da matsalaloli, babu wanda ya kula shi don haka ya dauki makami.

"Da muka tafi can suka ga akwai wanda zai saurare su, sun shirya yin sulhu, sun fada mana matsalolinsu kuma a shirye suke so koma cikin gari. A wannan halin, ban ga dalilin da yasa gwamnati ba za ta yi sulhu da su ba."

KU KARANTA: Irabor: Ƴan Boko Haram 500 Suna Gidan Yari, Wasu Za Su Shafe Shekaru 60 a Ɗaure

Gumi ya ce idan ba a nuna musu cewa babu abinda zai same su ba idan sun koma cikin mutane, ba za su ajiye makamansu ba.

Malamin addinin ya ce a yi musu afuwa kamar yadda aka yi wa tsagerun Neja Delta.

"Idan ba a nuna musu cewa babu abinda zai same su ba idan sun koma cikin gari, ba za su bar makamansu. Hakan yasa na nemi a musu afuwa kamar yadda aka yi wa yan Niger Delta.

"Ba laifi na ke hallastawa ba, abinda suka yi laifi ne. Amma suna garkuwa da mutane ne domin samun kudi su sake siyan makamai su kare kansu."

A wani labarin daban, hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, a ranar Litinin ta kama fitaccen mai wakokin yabon Annabi Muhammadu SAW, Bashir Dandago.

An kama shi ne kan zargin fitar da wakar da hukumar ta ce na iya tada fitina, da ta ce ya zagi malamai a jihar Kano kan matayarsu game da rikicin Sheikh AbdulJabbar Kabara.

Shugaban hukumar, Ismail Na'abba Afakallah ya tabbatarwa Daily Trust kamun.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel