Babu rashin jituwa tsakanin Buhari da babban amininsa Tinubu, duk aikin yan jarida ne: Fadar shugaban kasa

Babu rashin jituwa tsakanin Buhari da babban amininsa Tinubu, duk aikin yan jarida ne: Fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasa ta yi watsi da rahotannin cewa akwai rashin jituwa tsakanin shugaba Muhammadu Buhari da babban jigon jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

A jawabin da mai magana da yawun shugaban, Garba Shehu, ya saki ranar Laraba, ya ce akwai alaka mai karfi tsakanin Buhari da Tinubu musamman wajen ganin cigaban jam'iyyar All Progressives Congress, APC.

A cewar Garba Shehu, rahotannin da ake yadawa cewa akwai rashin jituwa tsakanin Buhari da Tinubu, aikin wasu miyagin yan jarida ne.

"Fadar shugaban kasa na son bayyana cewa babu rashin jituwa tsakanin shugaba Muhammadu Buhari da babban amininsa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu," cewar Garba Shehu.

"Rahotannin cewa akwai rashin jituwa tsakanin shugabannin biyu karya ne, aikin wasu miyagun yan jarida ne."

"Idan Asiwaju ba ya yawan zuwa fadar AsoRock Villa, ai don shi ba Minista bane."

Babu rashin jituwa tsakanin Buhari da Tinubu, duk aikin yan jarida ne: Fadar shugaban kasa
Babu rashin jituwa tsakanin Buhari da Tinubu, duk aikin yan jarida ne: Fadar shugaban kasa Credit: Fadar shugaban kasa
Source: UGC

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel