Ina durkusawa tare da mika kai ga mijina - Shugabar kasar Tanzania ta fadawa Mata a bidiyo

Ina durkusawa tare da mika kai ga mijina - Shugabar kasar Tanzania ta fadawa Mata a bidiyo

- Samia Suluhu ta ce mika wuya a gaban mijinta ba kaskanci bane face soyayya

- Shugabar kasar Tanzania mace ta farko ta fadi haka ne a lokacin da take mataimakiyar marigayi ubangidanta John Pombe Magufuli

- Yadda daidaiton jinsi ke shafar aure musamman ga mata na ci gaba da zama abin tattaunawa tsakanin kungiyoyin al'umma daban-daban

Wani bidiyo ya bayyana a shafukan sada zumunta wanda ke nuna Shugaba Samia Suluhu ta Tanzania tana cewa ba ta da wata matsala wajen mika wuya ga mijinta.

An ga bidiyon a shafin Twitter na wani mai suna @Goddieh_njihia wanda ya bayyana cewa mace ta farko da ta zama shugabar Tanzania abin kauna ce saboda kalamanta.

KU KARANTA KUMA: Kyawawan hotunan sarakuna 3 masu karancin shekaru a Najeriya da cikakken

Ina durkusawa tare da mika kai ga mijina - Shugabar kasar Tanzania ta fadawa Mata a bidiyo
Ina durkusawa tare da mika kai ga mijina - Shugabar kasar Tanzania ta fadawa Mata a bidiyo Hoto: mybrytfmonline.com; moderndiplomacy.eu
Asali: UGC

A cewarta, daga cikin rawar da suke takawa a gidan aure, ya kamata mata su mika wuya ga maza a matsayin nauyin kauna yayin da suma maza suke nuna musu kaunarsu.

Kalli bidiyon a kasa:

Kalmomin nata da aka fassara sun ce:

"Wasu daga cikinku za su ce daidai muke a dukkan bangarori, A'a! Wannan ba shi ne matsayin da ya dace ba. Ko da a matsayina na mataimakiyar shugaban kasa, zan durkusa a gaban mijina. Ba wai ina durkusawa saboda na kasa ba, ina yin hakan ne saboda so da kauna."

Binciken da Legit.ng ta gudanar, ya nuna cewa Samia Suluhu ta fadi haka ne a lokacin da take mataimakiyar shugaban kasa ga tsohon ubangidanta kuma wanda ya gabace ta, John Pombe Magufuli.

KU KARANTA KUMA: Zulum da sauran gwamnoni 4 da tsageru suka taba kaiwa hari a Najeriya

Batun daidaiton jinsi da yadda ake aiwatar da shi cikin aure musamman ga mata na ci gaba da zama abin tattaunawa tsakanin ƙungiyoyin al'umma daban-daban.

A wani labarin, Sulaiman Mohammad, kanin Abubakar Mohammed, marigayin sojan saman Nigeria, NAF, ya yi bayanin abinda ya sa ya auri matar da aka saka wa rana da kaninsa, makonni biyar bayan rasuwar kanin.

Abubakar na cikin sojojin da suka kwanta dama sakamakon artabu da suka yi da yan bindiga a Ungwan Laya da ke kusa da Birnin Gwari a ranar 13 ga watan Fabrairu.

Ya rasu ana sati uku daurin aurensa da Hajara, wadda tuni ya wallafa hotunan kafin aurensu a dandalin sada zumunta.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel