Dole ku shafa mana lafiya a 2023, PDP ta aika sakon gargadi ga APC

Dole ku shafa mana lafiya a 2023, PDP ta aika sakon gargadi ga APC

- Jam’iyyar PDP ta yi raddi kan kalaman da APC ta yi cewa za ta kwashe shekara 26 tana mulkin kasar

- Kakakin PDP Kola Ologbondiyan ya ce ‘yan Najeriya sun shirya tsaf domin fatattakar jam’iyya mai mulki a zaben 2023

- Shugaban jam’iyyar na riko kuma gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ne ya ce APC za ta ci gaba da mulki ranar Talata

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yi raddi a kan ikirarin da jam’iyyar APC mai mulki tayi na cewa tana da niyyar ci gaba da mulki a matakin tarayya na akalla shekaru 26.

A wata sanarwa daga kakakinta, Kola Ologbondiyan, PDP ta ce manufar APC adawa ce kai tsaye ga 'yan Najeriya, wadanda tuni suka "cimma matsaya don korarsu daga mulki a 2023".

KU KARANTA KUMA: Manyan kasashe 17 mafi farin ciki a Afirka a 2021, Najeriya ce ta karshe

Dole ku bar mulki a 2023, PDP ta aika sakon gargadi ga APC
Dole ku bar mulki a 2023, PDP ta aika sakon gargadi ga APC Hoto: @officialKolaO/Twitter, Femi Adesina/Facebook
Source: UGC

Jam’iyyar ta PDP ta kuma bayyana ikirarin da APC ta yi na yin rajistar ‘yan Najeriya miliyan 36 a matsayin wani shirme na siyasa da ikirarin wofi, wanda a cewarta babu wani tasiri da zai yi ga ‘yan Najeriya, Channels TV ta ruwaito.

PDP ta ce tana sane da cewa Shugaban kwamitin rikon karya na APC ta kasa, Gwamna Mai Mala Buni ya yi irin wannan “ikirarin ne bisa karfin da APC ke ganin tana da shi kan hukumar zabe da fannin shari’a da gayyato bata-gari daga wasu kasashe domin su taimaka mata wajen dagula lamura a lokacin zabe mai zuwa.”

Ya kara da cewa kalaman Buni na nufin ‘yan Najeriya su nade hannu su ci gaba da zama cikin kunci da talauci da yunwa da rashin tsaro, da ukuba na karin shekaru 26.

Ologbondiyan ya kara da cewa "wannan rashin tausayi da nuna halin ko in kula ne da bai kamata ‘yan Najeriya su nade hannu su zuba ido da ci gaba da zama cikin wannan halin ba."

KU KARANTA KUMA: Ina durkusawa tare da mika kai ga mijina - Shugabar kasar Tanzania ta fadawa Mata a bidiyo

A wani labarin, dattijon Arewa kuma dan majalisar dattawa daga Nassarawa Sanata Abdullahi Adamu, ya ce ana kokarin fakewa da sunan hare-haren da ake zargin makiyaya na kaiwa wasu jihohin kasar ne domin raba kan al'ummar arewa.

Yayin wata hira da BBC Sanatan, ya ce rikicin ya samo asali ne sakamakon toshe hanyoyi ko burtalin da suke bi, da kuma dazukan da aka kebe saboda kiwo, sannan aka gagara samar da wani shiri don ganin sun gudanar da harkokinsu.

Ya jaddada cewa, matukar ana son kawo karshen matsala, to dole ne gwamnati ta fahimci hadarin da ke cikin bari ana yin kiwo sakaka a fili, hasalima idan ta fahimci haka ya kamata ta samarwa makiyaya wata hanya da za su rika gudanar da harkokinsu.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit.ng

Online view pixel