Gara Gwamnatin Abacha Da Na Buhari, Dr Obadiah Mailafia

Gara Gwamnatin Abacha Da Na Buhari, Dr Obadiah Mailafia

- Dr Obadiah Mailafia, tsohon mataimakin bankin CBN ya ce gara mulkin Abacha da na Buhari

- Mailafia ya kuma yi ikirarin cewa manyan kasashen duniya da ke son tarwatsa Nigeria ne suka jefa kasar cikin halin rashin tsaro

- Mailafia ya yi wannan jawabin ne yayin hirar da aka yi da shi a wani shirin siyasa a gidan talabijin

Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Nigeria, CBN, Dr Obadiah Mailafia a ranar Laraba ya yi zargin cewa kasashe masu karfi na duniya suna kokarin tarwatsa Nigeria.

A zamanin yanzu, kasashe mafi karfi a duniya a cewar Wikipedia sune Amurka, Rasha, China da Tarayyar Kasashen Turai (European Union).

Gara Gwamnatin Abacha Da Na Buhari, Dr Obadiah Mailafia
Gara Gwamnatin Abacha Da Na Buhari, Dr Obadiah Mailafia. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Jerin Ƙasashen Duniya 10 Mafi Hatsarin Zama a Shekarar 2021

Har wa yau, a hirar da aka yi da shi a shirin Sunrise Daily a Channels Television, Mailafiya ya ce ba a taba samun gwamnati mai muni a kasar ba irinta Shugaba Muhammadu Buhari.

Da ya ke kwatanta gwamnatin Buhari da na Abacha, Mailafia ya ce gara mulkin Abacha da na Buhari.

"Wannan bai taba faruwa ba. Wannan ne lokaci mafi muni a Nigeria. Ba za ka iya kwatanta wannan da zamanin Abacha ba; Zamanin Abacha abin yabawa ne idan aka kwatanta da yanzu. Kana tunanin Abacha zai amince da abinda ke faruwa a yanzu? Ba za ka iya tafiya a mota ba, ana kashe-kashe a ko ina, ana lalata kayayyaki."

Duk dai a kan tsaro, Mailafia ya ce, "Kasashe masu karfin iko a duniya suna son tarwatsa Nigeria kuma abinda suka yi shine sun samu wasu mutane suka fada musu. 'An haife ku domin ku mulki sauran mutane'. Akwai abinda tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo ya kira 'Fulanisation' wato tursasa addini daya a kan sauran."

KU KARANTA: Hotunan Sabon Katafaren Gidan Da Ɗan Uwan Buhari Ya Gina A Abuja

Ya kara da cewa kasashen duniyan sun daure ma wasu cikin mutane gindi su rika kashe-kashe da cin zarafin sauran mutane kuma su ke basu makamai.

A wani labarin daban, hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, a ranar Litinin ta kama fitaccen mai wakokin yabon Annabi Muhammadu SAW, Bashir Dandago.

An kama shi ne kan zargin fitar da wakar da hukumar ta ce na iya tada fitina, da ta ce ya zagi malamai a jihar Kano kan matayarsu game da rikicin Sheikh AbdulJabbar Kabara.

Shugaban hukumar, Ismail Na'abba Afakallah ya tabbatarwa Daily Trust kamun.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel