Bidiyon Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi yana nuna kwarewarsa a harkar rawa
- Gwamna Bello na jihar Kogi ya haddasa cece-kuce yayin da sabon bidiyon sa na motsa jiki ya bayyana a yanar gizo
- An gano gwamnan na jihar Kogi a cikin bidiyon yana tikar rawa yayinda yake sauraron wakar hausa
- Tuni bidiyon ya haifar da martani daga 'yan Najeriya a shafukan sada zumunta
Duk da tarin ayyukan da ke gabansa a matsayinsa na gwamnan jihar Kogi, a koda yaushe Yahaya Bello ya kan ware lokaci don motsa jiki.
Hotunan gwamnan da dama da ake wallafawa a yanar gizo wadanda ke nuna shi yana wasan dambe ko motsa jikinsa a dakin motsa jiki sun tabbatar da jajircewarsa wajen kula da lafiyarsa.
A cikin wani sabon bidiyon gwamnan jihar Kogi da Legit.ng ta gani a shafin Twitter, an ganshi a dakin motsa jiki yana nuna kwarewarsa a harkar rawa.
KU KARANTA KUMA: Sojoji zasu kafa aikin sintiri a Tyomu bayan harin da aka kaiwa Ortom
Nwa Mazi Ogbonna ™, @ Chubalus16, ne ya wallafa bidiyon a shafin Twitter a ranar Litinin, 22 ga Maris, tare da taken:
"Yahaya Bello a 2023. Ya ba da mamaki!"
Bidiyon ya haifar da wasu martani a dandalin sada zumunta. Duba wasu a kasa:
Alkasim Abdulkadir, @alkayy, ya ce:
"Motsa jiki ko? Tsayawa takarar shugaban kasa ba tseren mita 100 bane."
CHUBI, @_ELIGEMS, ya ce:
"Muna bukatar kasancewa cikin koshin lafiya domin mu iya tafiyar da kasar yadda ya kamata"
Khalid, @ carliid, @ Chubalus16, ya ce:
”Wani soja ya je yayi kyakkyawan aiki na fansar mutuncin kayan soji. Wannan Yahaya Bello yana bata sunan kayan sojojin."
KU KARANTA KUMA: Yaro dan shekara 13 ya burge mutane da dama a shafukan sada zumunta bayan ya kera abin hawa da kwalin sabulu
A wani labarin, Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya ce idan aka gaza kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya, ba za a yi zaben 2023 ba.
Ortom ya bayyana hakan ne ranar Talata yayinda ya ziyarci shugaba Muhammadu Buhari a fadar Aso Villa, Abuja, rahoton Channels TV.
Yayin hira da manema labarai bayan ganawarsu, Gwamna Ortom ya bayyana cewa kasar nan na cikin wani muguwar hali idan ba'a magance matsalar tsaro ba.
Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.
Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.
Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.
Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411
Asali: Legit.ng