Sojoji zasu kafa aikin sintiri a Tyomu bayan harin da aka kaiwa Ortom

Sojoji zasu kafa aikin sintiri a Tyomu bayan harin da aka kaiwa Ortom

- Rundunar sojoji zata kafa aikin sintiri a Tyomu bayan harin da aka kaiwa Ortom

- Kwamandan rundunar Operation Whirl Stroke (OPWS), Manjo Janar Adeyemi Yekini ne ya bayyana hakan

- Ya kuma jaddada cewa zasu tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihohin Benue, Taraba da Nasarawa

Kwamandan rundunar Operation Whirl Stroke (OPWS), Manjo Janar Adeyemi Yekini, ya ce za a kafa aikin sintiri a yankin da ‘yan bindiga suka kaiwa Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwe hari yan kwanaki da suka gabata.

An kai wa Ortom hari ne a ranar Asabar a Tyomu, wata karkara da ke wajen Makurdi yayin da yake dawowa daga gonarsa.

Yekini, a ranar Talata, yayin da yake jawabi ga manema labarai a Makurdi a kewayen Tyomu da ke kusa da kogin Benuwai, ya ce tura karin sojoji zuwa wurin zai hana ci gaba da kai hare-hare, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Sojoji zasu kafa aikin sintiri a Tyomu bayan harin da aka kaiwa Ortom
Sojoji zasu kafa aikin sintiri a Tyomu bayan harin da aka kaiwa Ortom Hoto: thedefensepost.com
Source: UGC

KU KARANTA KUMA: Yaro dan shekara 13 ya burge mutane da dama a shafukan sada zumunta bayan ya kera abin hawa da kwalin sabulu

"Za mu kafa sintiri a wannan yankin," in ji shi.

Kwamandan rundunar ya kuma ce OPWS na aiki tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro don tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihohin ta uku na; Benue, Taraba da Nasarawa.

Ya kara da cewa: “Mun kawo ku nan ne domin mu tabbatar muku da cewa babu wasu masu laifi a nan.

“Mun kakkabe yankin a baya.

"Mun amsa cikin gaggawa don ceto lokacin da muka samu kiran damuwa na gwamnan kuma mun ji makiyan sun koma cikin daji.

“Mun fatattake su. Mun kone wuraren buyarsu."

KU KARANTA KUMA: Ya samu kyautar N20K daga tsohon abokinsa da suka yi shekaru 6 suna zuwa makaranta kan alkhairin da yayi masa

A gefe guda, Gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, a ranar Litinin ya roki ‘yan Najeriya da kada su sanya siyasa a harin da aka kai masa, yana mai cewa hakan ya wuce siyasar bangaranci.

Gwamnan a ranar Asabar ya ce kimanin makiyaya 15, wadanda ke sanye da bakaken kaya, sun bude masa wuta tare da mukarrabansa a gonarsa, inda ya yi ikirarin cewa sai da ya yi tafiyar kimanin kilomita 1.5 don tsiratar da rayuwarsa.

Amma da yake zantawa da manema labarai bayan taron Majalisar Tsaro ta Jihar a New Banquet Hall na gidan Gwamnati, Makurdi, a ranar Litinin, Ortom ya ce ba shi ne gwamna na farko da aka kaiwa hari ba a ‘yan kwanakin nan.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit.ng

Online view pixel