Ba za'ayi zaben 2023 ba idan aka gaza magance matsalar tsaro, Gwamnan Benuwe

Ba za'ayi zaben 2023 ba idan aka gaza magance matsalar tsaro, Gwamnan Benuwe

- Jim kadan bayan ganawarsa da Buhari, Ortom ya gargadi gwamnatin APC

- Kwana uku bayan harin da aka kai masa, Ortom ya gana da shugaban kasa a Abuja

- A cewarsa, wajibi ne a magance matsalar tsaro da gaggawa

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya ce idan aka gaza kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya, ba za a yi zaben 2023 ba.

Ortom ya bayyana hakan ne ranar Talata yayinda ya ziyarci shugaba Muhammadu Buhari a fadar Aso Villa, Abuja, rahoton Channels TV.

Yayin hira da manema labarai bayan ganawarsu, Gwamna Ortom ya bayyana cewa kasar nan na cikin wani muguwar hali idan ba'a magance matsalar tsaro ba.

Ya yi Alla-wadai da yadda ake bari wasu yan tsiraru suke cin karansu ba babbaka a kasar nan inda yake kira ga gwamnatin tarayya tayi gaggawan hukunta duk wanda aka kama.

Wannan ziyara ya biyo bayan harin da aka kaiwa Gwamnan karshen makon da ya gabata a cikin garin Makurdi.

Gwamnan ya jaddada cewa kimanin yan bindiga 15 wadanda yayi zargin makiyaya ne sun bude masa wuta yayinda yake hanyar zuwa gonarsa.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe shugaban wasu Fulani a jihar Kaduna

Ba za'ayi zaben 2023 ba idan aka gaza magance matsalar tsaro, Gwamnan Benuwe
Ba za'ayi zaben 2023 ba idan aka gaza magance matsalar tsaro, Gwamnan Benuwe Credit: @channelstv
Asali: Twitter

DUBA NAN: Kwara: Rikici kan hijabi ya haɓaka, ƴan daba sun kai hari makarantu da kantuna

A bangare guda, rundunar yan sanda ta kama masunta yan kabilar jukun su uku kan zargin hannu cikin harin da aka kai wa tawagar Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue a hanyar Tyo Mu a Makurdi.

Mai bawa gwamnan shawara kan tsaro, Kwanel Paul Hemba, ya tabbatar da hakan yayin da ya ke zagayawa da manema labarai wurin da aka kai harin a ranar Talata.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng