Yaro dan shekara 13 ya burge mutane da dama a shafukan sada zumunta bayan ya kera abin hawa da kwalin sabulu
- Wani matashin dan Najeriya ya sanya jama’a tofa albarkacin bakunansu da fasaharsa wanda aka wallafa a shafin Twitter
- Yaron mai shekaru 13 ya kera abin hawa da kwalin sabulu, kuma ba da dadewa ba fasahar ta shahara bayan an yada ta a yanar gizo
- A 'yan kwanakin nan, kananan yara a kasar suna ta baje kolin baiwarsu ga duniya gaba daya
Wani dan Najeriya mai shekaru 13 ya sha ruwan yabo a shafukan sada zumunta bayan ya kera motar wasan yara da kwalin sabulu.
Matashin yaron ya kara tabbatar da cewa Najeriya gida ce ga yara masu hazaka da yawa waɗanda a shirye suke su mamaye duniya da fasaharsu.
KU KARANTA KUMA: Ya samu kyautar N20K daga tsohon abokinsa da suka yi shekaru 6 suna zuwa makaranta kan alkhairin da yayi masa
Da yake wallafa hoton motar a shafinsa, @OmoGbajaBiamila ya rubuta:
"Wannan yaro dan shekara 13 mai hazaka ya kera wannan motar tun daga farko da kwalin sabulu. Dan Allah a yada don duniya ta ga gagarumin fasaharsa ..."
Idan aka kula da hazikancinsa sosai, yaron mai shekaru 13 zai iya gina abin da Abdulmumin Adinoyi Taofiq ya gina kwanaki.
A tuna cewa Abdulmumin ya sa mabiya kafofin sada zumunta magana bayan ya gina karamin jirgin sama kuma ya tashi.
Yaron ya yada wani bidiyo a shafukan sada zumunta inda aka ga ya tashi 'jirgin' tare da na'urar sarrafa shi.
An jiyo sauran samari da suka hallara don shaida abin da ya faru suna ta ihu cikin farin ciki yayin da jirgin ya tashi sama.
KU KARANTA KUMA: Tukuicin sauya sheka:Omisore, Bankole, Dogara sun samu manyan mukamai a APC
Abdulmumin ya rubuta: "A ƙarshe na sanya jirgina ya tashi, bayan shekaru da yawa ina ƙoƙari. Na ari batirin Lipo daga hannun Victor Moses. Har yanzu ina buƙatar ɗaya ta kaina duk da cewa, ya kai 15k. #Taohan."
A wani labari na daban, wani ‘dan mai ba uwargidar shugaban Najeriya, Aisha Muhammadu Buhari, ya fito da hotunan wata mota mai tsada da ya mallaka.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wani yaron Dr. Hajo Sani, ya saye wata mota wanda za ace ‘son kowa, kuma kin wanda ya rasa.’
Wannan Bawan Allah mai amfani da sunan Kingdibbo a shafinsa na Instagram, shi ne ya wallafa hotunan sabuwar amaryar da ya yi.
Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.
Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.
Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.
Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411
Asali: Legit.ng