Rashin Tsaro: Gwamnatin Katsina ta bada umarnin buɗe makarantun kwana

Rashin Tsaro: Gwamnatin Katsina ta bada umarnin buɗe makarantun kwana

- Gwamnatin jihar Katsina ta bada umarnin buɗe makarantun kwanan dake faɗin jihar daga ranar Laraba 24 ga watan Maris

- Sai dai gwamnatin tace duk daliban su koma makarantun dake kusa da garuruwan da suke zaune

- Ta kuma bada umarnin buɗe wasu makarantun guda biyar daga ranar 28 ga watan Maris

Gwamnatin jihar Katsina ta umarci ɗalibai mata dake yin makarantun kwana a faɗin jihar da su koma makarantun dake kusa da su daga ranar Laraba 24 ga watan Maris.

Kuma gwamnatin ta bada umarnin buɗe wasu makarantun guda biyar dake jihar daga ranar Litinin 28 ga watan Maris ɗin da muke ciki, kamar yadda Punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Zamu Kama Duk Wani Matafiyi mai dauke da Gwajin COVID19 na Bogi, NCDC

Makarantun da umarnin ya shafa sun haɗa da; makarantar sakandiren gwamnati dake Malumfashi (Unity), SUNCAIS Katsina, Makarantar mata ta gwamnati dake Dutsin-Tsafe, makarantar sakandiren mata Dutsinma, makarantar kurame dake Malumfashi, da kuma makarantar makafi Katsina.

Rashin Tsaro: Gwamnatin Katsina ta bada umarnin buɗe makarantun kwana
Rashin Tsaro: Gwamnatin Katsina ta bada umarnin buɗe makarantun kwana Hoto: @Governormasari
Asali: Twitter

A jawabin da mai magana da yawun ma'aikatar ilimin jihar, Sani Suleiman ya yi a madadin kwamishinan ilimi, a ranar Litinin da yamma yace:

"Kamar yadda ƙa'idojin komawa makarantu ya tanadar a jihar Katsina, mai girma gwamnan jihar, Aminu Bello Masari, ya umarci ɗaukacin ɗalibai mata dake karatu a makarantun kwana na jihar su koma makarantun jeka ka dawo na kusa da garin da suke zaune daga ranar 24 ga Maris."

"Sannan kuma gwamnatin ta bada umarnin buɗe waɗannan makarantun, kamar haka; makarantar sakandiren gwamnati dake Malumfashi (Unity), SUNCAIS Katsina,"

"Makarantar mata ta gwamnati dake Dutsin-Tsafe, makarantar sakandiren mata Dutsinma, makarantar kurame dake Malumfashi, da kuma makarantar makafi Katsina." a cewarsa.

MAKARANTA ANAN: Kada ku yarda a kafa dokar halasta sanya Hijabi a makarantu, CAN ga yan majalisa Kiristoci

"Dole ne ɗalibai, malamai, da kuma masu kawo ziyara su tabbata suna bin dokokin kare yaɗuwar cutar korona" inji shi.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, an rufe makarantun ne a watan Disamban shekarar data wuce bayan sace ɗalibai 344 da wasu yan bindiga sukayi a makarantar sakandiren kwana, Ƙanƙara.

Duk da an saki ɗaliban kwana shida da kama su amma gwamnati ta ɗauki matakin kulle makarantun ne don gudun ƙara faruwar haka.

Sai dai mafi yawancin makarantun sun koma aiki a watan da ya gabata.

A wani labarin kuma Kada ‘yan Najeriya su sanya siyasa a harin da aka kai mun, in ji Ortom

Gwamna Samuel Ortom ya roki da kada su siyasantar da harin da aka kai masa, yana mai cewa hakan ya wuce siyasar bangaranci.

Ortom ya bayyana cewa ba shine gwamna na farko da aka kaiwa hari ba kuma cewa yana iya zama wani a gaba.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77.

Asali: Legit.ng

Online view pixel