'Yan bindiga sun kashe shugaban wasu Fulani a jihar Kaduna

'Yan bindiga sun kashe shugaban wasu Fulani a jihar Kaduna

- Wasu 'yan bindiga sun hallaka wani shugaban Fulani a yankin Doka dake jihar Kaduna

- Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwarsa, ta kuma yi Allah wadai da lamarin

- Hakazalika gwamnatin jihar Kaduna ta jajanta tare da yi wa iyalan mamacin ta'aziyya

Lawal Musa, shugaban al'ummar Fulani a karamar hukumar Kajuru da ke Kaduna, ya rasa ransa sakamakon wani hari da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai, The Cable ta ruwaito.

Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro na cikin gida a Kaduna, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

Musa, wanda aka fi sani da suna "Alhaji Maijama'a", an ba da rahoton kashe shi a daren Lahadi.

Kwamishinan ya bayyana cewa Musa yana kan babur tare da dan uwansa, kwasam ‘yan bindigan suka bude musu wuta.

"Wasu 'yan bindiga sun kashe wani shugaban al'ummar Fulani a yankin Doka da ke karamar hukumar Kajuru, Alhaji Lawal Musa, wanda aka fi sani da Alhaji Maijama'a, a daren ranar Lahadi," in ji sanarwar.

KU KARANTA: A karkashin mulkin Tinubu ne kadai Najeriya za ta daidaita, in ji wasu manyan arewa

'Yan bindiga sun kashe shugaban wasu Fulani a jihar Kaduna
'Yan bindiga sun kashe shugaban wasu Fulani a jihar Kaduna Hoto: vanguardngr.com Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

“Jami’an tsaro ne suka sanar da wannan ga Gwamnatin Jihar Kaduna a ranar Lahadi.

"Alhaji Lawal Musa ya kasance shugaban al’ummar Fulani a yankin Doka da ke karamar hukumar Kajuru wanda ya yi aiki kafada da kafada da sauran shugabannin al’ummar wajen cimma nasarar kokarin samar da zaman lafiya a yankin.

“Wasu 'yan bindiga sun kashe Alhaji Lawal Musa a mazauninsa, a gaban danginsa. Yana kan babur tare da babban wansa, Alhaji Gide Musa, lokacin da wasu mahara suka bude musu wuta.

"Alhaji Gide Musa ya tsere da raunin harbin bindiga, yayin da ‘yan bindigan suka rike Alhaji Maijama’a suka yi masa yankan rago har lahira.

“Tuni aka binne shi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Dan uwan ​​nasa yana jinya a wani asibiti da ba a bayyana ba. ”

Aruwan ya bayyana gudummawar da Musa ya bayar a matsayin "kayan aiki don sake bude kasuwar mako-mako ta Doka, sake dawo da hada-hada cikin lumana a wuraren ibada da aka yi watsi da su da kuma sake dawo da kiwo da noma a babban yankin Doka"

Kwamishinan ya kara da cewa Nasir El-Rufai, gwamnan jihar ta Kaduna, ya yi Allah wadai da lamarin kuma ya aike da ta’aziyya ga iyalan mamacin.

Haka kuma an ce El-Rufai ya bayyana marigayi shugaban na Fulani a matsayin "shugaba nagari kuma mai kishin zaman lafiya".

KU KARANTA: Kamfanin MTN ya bai wa Najeriya gudunmawar alluran Korona guda 300,000

A wani labarin, Iyayen daliban da aka sace na Kwalejin Noma da Ilimin Gandun Daji ta Tarayya da ke karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna, sun bada wa’adin awanni 48 ga Gwamnatin Jiha da ta Tarayya don ceton ’ya’yansu.

Wannan ya kasance daidai lokacin da iyayen, cikin kuka, suka yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya, Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya, Kungiyar Ma’aikatan Jami’o’i da shugabannin duniya da su tabbatar da hanzarta kubutar da 'ya’yansu daga 'yan bindiga.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel