Iyayen dalibai sun bai wa El-Rufa'i wa'adin awanni 48 ya dawo musu da 'ya'yansu

Iyayen dalibai sun bai wa El-Rufa'i wa'adin awanni 48 ya dawo musu da 'ya'yansu

- Iyayen daliban da aka sace a wata kwaleji a Kaduna sun ba da wa'adi ga gwamnati ta ceto yaransu

- Iyayen sun koka kan yadda gwamnati ke jinkiri wajen jajircewa don ceto yaran nasu da aka sace

- Sun kuma tuhumi gwamnatoci da nuna halin ko-in-kula da sace daliban da aka yi a kwanan nan

Iyayen daliban da aka sace na Kwalejin Noma da Ilimin Gandun Daji ta Tarayya da ke karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna, sun bada wa’adin awanni 48 ga Gwamnatin Jiha da ta Tarayya don ceton ’ya’yansu.

Wannan ya kasance daidai lokacin da iyayen, cikin kuka, suka yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya, Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya, Kungiyar Ma’aikatan Jami’o’i da shugabannin duniya da su tabbatar da hanzarta kubutar da 'ya’yansu daga 'yan bindiga.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Gobara ta yi kaca-kaca da babbar kasuwar Katsina

Iyayen dalibai sun bai wa El-Rufa'i wa'adin awanni 48 ya dawo musu da 'ya'yansu
Iyayen dalibai sun bai wa El-Rufa'i wa'adin awanni 48 ya dawo musu da 'ya'yansu Hoto: blueprint.ng
Asali: UGC

Yayin da suke jawabi ga taron manema labarai a ranar Litinin, iyayen sun ce hukumar makarantar ko gwamnatoci ba su yi musu bayani ba game da kokarin kubutar da yaransu, jaridar Punch ta ruwaito.

A cewarsu, shirun da mahukuntan da abin ya shafa suka yi ya yi tsawo, saboda haka sun ba da wa'adin awanni 48 da ya kamata a ceci yaransu.

Iyayen sun kuma yi kuka da nuna halin ko-in-kula da gwamnatocin ke nunawa game da batun yaran da wasu ‘yan bindiga suka sace su kwanaki 12 a kwalejin.

Sun yi tambaya kan dalilan da ke haifar da rashin sha'awar gwamnatoci don ceton 'ya'yansu da suke rabi tsirara lokacin harin.

A cewarsu, gwamnatoci daban-daban sun yi hanzari lokacin da irin wannan ya faru a jihohin Zamfara, Katsina da Neja, suna tuhumar me yasa na jihar Kaduna ya bambanta.

KU KARANTA: A karkashin mulkin Tinubu ne kadai Najeriya za ta daidaita, in ji wasu manyan arewa

A wani labarin daban, Wani shugaban ‘yan bindiga a jihar Zamfara, Shehu Rekeb, ya ce kungiyar sa ta haramta ayyukan hakar ma’adanai a duk wuraren da su ke aiki.

Gwamnatin Tarayya ta alakanta ayyukan masu hakar ma'adanai da 'yan bindiga, kuma ta ba da umarnin dakatar da hakar ma'adanai a jihar. Amma a zantawarsa da Daily Trust, Rekeb ya ce tun kafin umarnin na gwamnatin tarayya, kungiyar tasa ba ta barin masu hakar ma’adanai a wuraren da suke da karfi.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel