Burutai da sauran hafsoshin tsaro za su bayyana a gaban majalisa kan batun kudin makamai

Burutai da sauran hafsoshin tsaro za su bayyana a gaban majalisa kan batun kudin makamai

- Majalisar wakilai a Najeriya ta gayyaci hafsoshin tsaron kasa da su bayyana a gaban majalisar

- Gayyatar ta biyo bayan kamalan mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaro a makon jiya

- Munguno ya bayyana cewa, basu san inda kudin sayen wasu makamai suka shiga ba, wanda ya jawo cece-kuce

Kwamitin gaggawa da aka kafa domin binciken kudaden sayen makamai da amfani da su na Majalisar Wakilan Najeriya ya gayyaci hafsoshin tsaro da sauran shugabannin tsaron kasar.

Shugabannin tsaron za su yi bayani ne game da sayowa da kuma inda aka kwana wajen rabawa da amfani da makaman da aka sayo din a gobe Litinin.

Jaridar Punch a ranar Asabar ta ruwaito cewa Kwamitin Tsaro na Majalisar ya gana da Ma'aikatar Tsaro kan kudi dala biliyan daya da aka ware don sayen makamai a 2017, wadanda daga cikinsu ne aka biya kudin jiragen Super Tucano guda 12 a Amurka.

KU KARANTA: Ya kamata a samu mataimakan shugaban kasa 2 a Najeriya, Yakubu Gowon

Burutai da sauran hafsoshin tsaro za su bayyana a gaban majalisa kan batun kudin makamai
Burutai da sauran hafsoshin tsaro za su bayyana a gaban majalisa kan batun kudin makamai Hoto: punchng.com
Source: UGC

Wannan bincike ya biyo bayan kalaman da mai bai wa Shugaba Buhari shawara kan tsaro Manjo Janar Babagana Monguno ya yi ne a hirarsa da BBC Hausa, inda ya ce ba su san inda kudin makaman suka shiga ba.

Kalaman nasa sun tayar da muhawara tsakanin 'yan Najeriya, ganin cewa ba wannan ne karon farko da aka zargi shugabannin tsaron da sace biliyoyin kudin makamai ba.

Shugaban kwamitin, Olaide Akinremi, ya fada wa Punch cewa bayan zamansu na farko sun yanke shawarar binciken kudaden makaman cikin shekara 10 da suka wuce kuma hafsoshin tsaron za su bayyana gaban majalisar a gobe Litinin.

An bayar da odar makaman ne a karkashin tsoffin hafsoshin tsaro, wadanda Buhari ya sauya a ranar 26 ga watan Janairu kuma ya maye gurbinsu da wasu.

KU KARANTA: Na yi nadama kwarai da gaske: Okupe ya nemi afuwa kan batun shugabanci Ibo

A wani labarin daban, Ofishin ONSA na mai ba shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro ya fito ya yi karin haske a a kan kalaman da ya yi a game da salwantar kudin makamai.

A wani jawabi da ONSA ya fitar, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya) ya ce ‘yan jarida sun rikada kalamansa bayan hirar da ya yi da BBC Hausa.

Legit.ng Hausa ta samu ganin wannan jawabi da Babagana Monguno ya yi, ya ce a hirar da aka yi da shi, babu inda ya nuna an yi awon-gaba da kudin makamai.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit

Online view pixel