Ubangiji da 'yan Najeriya ku Yafe min, Melaye yayi Nadamar Goyon Bayan Buhari a 2015

Ubangiji da 'yan Najeriya ku Yafe min, Melaye yayi Nadamar Goyon Bayan Buhari a 2015

- Sanata Dino Melaye yace gagarumar damfarar da aka yi a 2015 a fadin Afrika ita ce goyon bayan Buhari

- Melaye ya nemi gafarar Ubangiji tare da ta 'yan Najeriya a kan goyon bayan Buhari da yayi a 2015

- Kamar yadda yace, a da ya kasance makaho amma yanzu ya samu lafiya kuma yana ganin komai tangaran

Dino Melaye, tsohon sanatan da ya wakilci jihar Kogi ta yamma, yace babbar damfarar da ta taba faruwa a Afrika shine yadda aka goyawa Buhari baya ya samu shugabancin kasa a 2015.

Melaye ya sanar da hakan ne a ranar Juma'a yayin da ya bayyana a wani shiri na gidan talabijin na Channels.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, Melaye, wanda yanzu dan babbar jam'iyyar adawa ce ta PDP, ya bar jam'iyyar APC a shekarar 2018.

A yayin jawabi a shirin, ya mika ban hakurinsa ga 'yan Najeriya da ya goyi bayan Buhari a 2015 inda yace ya taba makancewa, amma yanzu yana gani.

KU KARANTA: Tsabar sharri na hada, na mannawa Ortom a 2018, Oshiomhole ya janye zarginsa

Gagarumar damfarar da aka taba a Afrika, Melaye yayi nadamar goyon bayan Buhari a 2015
Gagarumar damfarar da aka taba a Afrika, Melaye yayi nadamar goyon bayan Buhari a 2015. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sojin Najeriya sun sheke 'yan bindiga 2, sun cafke masu siyar da makamai a Kaduna

"Bari in fara da mika ban hakuri na ga Ubangiji, wanda ke mulkin duniya da kuma 'yan Najeriya a kan goyon bayan Buhari da nayi," yace.

"Tsarin Buhari na daga cikin babbar damfarar da ta taba faruwa a Afrika. Takarar Buhari ta 2015 ita ce gagarumar damfarar da aka taba kuma daga Afrika ta fito."

Jigon jam'iyyar PDP yace yana mamakin yadda har yanzu akwai masu goyon bayan shugaban kasan duk da al'amuran da ke faruwa a kasar nan.

A wani labari na daban, Isyaka Amao, shugaban dakarun sojin saman Najeriya yace rundunar sojin Najeriya ta shirya kakkabo 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane dake fadin kasar nan.

Shugaban yace sojojin sun kammala dukkan shirinsu na ganin bayan 'yan ta'addan da suka addabi kasar nan.

Jaridar The Cable ta ruwaito, ya sanar da hakan ne a ranar Laraba yayin wata ziyarar aiki da ya kai sansanin sojin saman Najeriya dake jihar Kaduna.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel