Wajabcin bayyana dukiyoyin ma’aikatan Banki: Sabon Shugaban EFCC ya yi daidai, Barista AlBashir Lawal Likko

Wajabcin bayyana dukiyoyin ma’aikatan Banki: Sabon Shugaban EFCC ya yi daidai, Barista AlBashir Lawal Likko

- Masanin dokokin Najeriya, Barista AlBashir Lawal Likko ya yi tsokaci a kan tsarin da hukumar EFCC ta fito da shi kan dukka ma'aikatan bankin kasar

- Dokar dai ta ce daga ranar 1 ga watan Yuni, ma'aikatan banki za su fara bayyana dukiyoyinsu da nauyin tattalin arzikinsu

- Barista Likko ya ce hakan ya yi daidai domin dai tun dama akwai wannan doka kawai dai bata aiki ne saboda yanayin kasar da ke bacci

Wani masani a ilimin dokokin Najeriya kuma lauya mai zaman kansa, Barista AlBashir Likko, ya goyi bayan kudirin sabon shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa na wajabtawa dukkan ma’aikatan bankin kasar bayyana dukiyoyinsu.

Kamar yadda Bawa ya bayyana, wannan dokar za ta fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Yuni na wannan shekarar.

Sai dai kuma, Barista Likko ya bayyana cewa wannan doka da Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ya kawo, ba sabuwa bace domin tun a 1986 aka kafa ta.

Wajabcin bayyana dukiyoyin ma’aikatan Banki: Sabon Shugaban EFCC ya yi daidai, Barista AlBashir Likko
Wajabcin bayyana dukiyoyin ma’aikatan Banki: Sabon Shugaban EFCC ya yi daidai, Barista AlBashir Likko
Asali: Original

Ya bayyana cewa kawai dai akwai wasu dokoki ne da dama da ba a amfani da su a kasar ta yadda idan aka yi sabon shugaba ya farfado da su sai mutane su kalle shi a matsayin sabon salo.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotu ta tsare Shugaban PDP mai shekaru 80 a Oyo kan kisan kai

A wata hira da Legit.ng Hausa, Barista AlBashir Lawal Likko ya ce:

“Alhamdulillahi dukkan wani tsari game da wata hukuma wanda gwamnatin tarayya ta kafa dangane da abun da ya shafi dokoki ko kuma aikata wani abu, musamman a wannan bangare na EFCC wacce ma’aikata ce wacce take kula da almundahana da kuma ta’annati dangane da abun da ya shafi harka na shige da fice na kudi ga ma’aikata ko kuma ma wadanda ba ma’aikata na gwamnati ba.

“Wannan doka ta 'Bank employee act declaration of assets 1986' ai ta dade kwarai da gaske, matsalar da muke fama da shi ita ce akwai dokoki sosai suna nan jinkin a nan kasar amma sakamakon baccin da kasar take yi sai dokokin suma suna bacci.

“Duk lokacin da aka samu wani shugaba ya dauko wani doka ya ce a’a ya kamata lallai wannan dokar a sata a cikin yanayin da za ta yi aikinta, sai mutane su dunga kallonta a hanyar kamar wani abu ne ya zo da shi sabo.

“Wannan dokar ba sabuwa bace, saboda doka ce wacce a yanzu idan ana magana yaron da aka haifa a shekara 1986 yanzu ai ya gama jami’a har ya je ma ya zama wani abu a tsarin rayuwarsa idan dai har ya samu kyakkyawar kulawa.

“Don haka wannan dokar ba sabuwa bace, abunda mutane suka kasa fahimta shine wato menene alakar dokar da kuma aikin da shi wannan shugaba na EFCC ya kawo.

“Bangaren EFCC sashi na 7(2) ya ba bangaren EFCC ko Shugaban EFCC dama na cewa su binciki duk wata almundahana wacce take da alaka da kudi koda ba ma’aikacin gwamnati bane.

“Saboda ita almundahana da take da alaka da kudi, ma’aikacin gwamnati na iya hada baki da wanda ba ma’aikacin gwamnati ba wajen boye kudi ko yin wata almundahana. Kamar yadda kuma suma ma’aikatan banki suma ana amfani da su ta bangarori da dama wajen boye kudi na gwamnati, ko kuma wajen boye wani kudi wanda koda ba na gwamnati ba amma dai kuma babu gaskiya a cikinsa akwai almundahana a ciki.

KU KARANTA KUMA: Yawan yaran da basa zuwa makaranta ya karu da miliyan 3 cikin watanni uku

"Idan muka kalla, shi sashi na 1(2) na waccan ita doka ta ‘bank employee act declaration’ ai ya fada cewa duk lokacin da aka ce ma’aikacin banki ya tsinci kansa a matsayinsa na ma’aikaci, lallai ne bayan an dauke shi aiki ya zo ya cika wata takarda wato fam kenan, wanda wannan fam din zai yi bayanin dukiyar da ya mallaka da nauyin tattalin arzikinsa.

"Toh idan ya cike wannan fam din, sashi na 14 ya ce sai ya kai wannan fam dinsa wajen sakataren gwamnatin tarayya wato SGF kenan, toh wannan ofishin ita ce ke da alhakin karbar wannan fam din nashi.

"Toh a cikin wannan dokar babu kuma inda dokar ta ce shi sakataren gwamnatin tarayyar shine kadai ko kuma wannan ofishin ne kawai zai iya karbar wannan fam din, ko kuma sanin me aka cike wannan fam din ko an cike daidai ko ba a cike daidai ba, ko anyi algush ko an boye wani abu.

"Toh shi kuma a bangaren EFCC tunda bincike suke yi a gaba daya abunda ya shafi almundahanar kudi, don haka sashi na 7(2) ya tabbatar da cewar EFCC tana da wannan karfin da ba wai a wannan bangaren ba har a koina."

A wani labari na daban, Michael Wetkas, wani shaidar hukumar yaki da rashawa ta EFCC, ya yi zargi tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido da karbar cin hanci daga hannun yan kwangila da ake bawa aiki a lokacin mulkinsa, rahoton The Cable.

A shekarar 2015, hukumar EFCC ta kama tsohon gwamnan tare da yaransa biyu, Aminu da Mustapha kan zargin almundahar kudade da rashawa.

Daga baya an gurfanar da su a wata kotun tarayya da ke Abuja.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel