Za a yiwa malaman addini alluran rigakafin Korona saboda su jawo hankalin mabiyansu
- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, zata hada hannu da malamai wajen gudanar allurar Korona
- Gwamnatin ta bayyana cewa, malaman za ai musu allurar a matsayin misali ga mabiyansu
- Tuni Sarkin Musulmi ya bai wa malamai umarnin su koma garuruwansu don wayarwa mutane kai
Shugaban Kwamitin Shugaban kasa (PTF) kan Korona kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Boss Mustapha, ya ce gwamnatin tarayya za ta tabbatar da damawa da shugabannin addinai wajen wayar da kan mabiyansu game da bukatar yin rigakafin Korona.
Mista Mustapha wanda yake magana a kashi na biyu na wayar da kan malamai da limamai kan allurar da hukumar NPHCDA ta shirya a Abuja, ya ce gwamnati za ta tabbatar da cewa shugabannin a dukkan matakai sun yi allurar.
Ya bayyana hakan a matsayin zama misali ga al'ummar da suke shugabanta, Daily Trust ta ruwaito.
KU KARANTA: Dalilan da suka sanya jihar Kano haramta sayar da lemon dan tsami
Ya yaba wa Malaman addinin Islama kan goyon bayan da suka ba shi, sannan ya kara da cewa a matsayinsu na shugabanni kuma masu kula da ka'idojin addini ya kamata su fadakar da mabiyansu cewa rigakafin yana da kyau da kuma tasiri
Ya kuma kafa hujja da cewa, Kungiyar Tarayyar Turai (EU) da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) duk sun tabbatar da ingancin allurar rigakafin.
Ya ce Najeriya na fatan yiwa kashi 70 na ‘yan kasarta allurar tsakanin shekarar 2021 da 2022.
Ministan Kiwon Lafiya, Dokta Osagie Ehanire, ya ce akwai bukatar a sake bai wa ‘yan Najeriya tabbaci kan lafiyar allurar, yana mai cewa dakatar da allurar ta AstraZeneca da wasu kasashe suka yi bai hana amfani da allurar ba.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), Muhammad Sa’ad, ya bukaci malaman da su koma yankunansu don tattauna lafiyar allurar.
KU KARANTA: 'Yan sanda sun sheke 'yan bindiga, sun kwato bindigogi da mota a Kaduna
A wani labarin daban, Hukumar kula da matasa masu yi wa kasa hidiman ta kammala shirye-shirye don ba da allurar rigakafin Korona ta AstraZeneca, ga dubunnan mambobin bautan kasar na Batch A 2021 wadanda yanzu haka ke kan aikinsu a dukkan sansanoni 37 a fadin kasar.
An samu labarin cewa hukumomin NYSC sun hadu da kwamitin shugaban kasa kan Korona a Abuja don amincewa sannan za su kuma hadu da Hukumar Kiwon Lafiya a Matakin Farko, wani sashe na Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta Tarayya kan shirin.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng