Buhari ya yi alkawarin ci gaba da tallafawa mata a fadin Najeriya

Buhari ya yi alkawarin ci gaba da tallafawa mata a fadin Najeriya

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari a Najeriya ya yi akawarin ci gaba da tallafawa mata a kasar

-Shugaban ya yabawa mata a gwagwarmayarsu ta kawo ci gaba da kyakkyawan suna ga Najeriya

- Hakazalika ya tabbatar da cewa, zai ci gaba da hannu da kungiyoyin da suka dace don damawa da mata

Shugaba Buhari ya ba da tabbacin cewa, Ma’aikatun Harkokin Mata da na Shari'a za su yi aiki tare da Majalisar Dokoki ta Kasa don tabbatar da cewa an gabatar da gyare-gyaren da suka dace a cikin ayyukan gyaran tsarin mulki da na zabe da ke gudana don tallafawa tafarkin mata.

Shugaban ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Juma’a yayin da yake jawabi a Fadar Gwamnati inda ya karbi bakuncin kungiyoyin kwadago na kasa da na duniya na Tallafin Cigaban Jinsi (SAGE) don tunawa da Ranar Mata ta Duniya shekarar 2021 (IWD).

Shugaban, wanda ya ce ya dukufa kwarai da gaske don ganin karuwar matan Najeriya a mukaman shugabanci a cibiyoyin kasa da na duniya, ya ba da tabbacin cewa za a kara samun saukin ba da bashi, kuma za a samar da karin sarari ga mata don shiga harkokin siyasa.

KU KARANTA: Za a yiwa malaman addini alluran rigakafin Korona saboda su jawo hankalin mabiyansu

Buhari ya yi alkawarin ci gaba da tallafawa mata a fadin Najeriya
Buhari ya yi alkawarin ci gaba da tallafawa mata a fadin Najeriya Hoto: ripplesnigeria.com
Asali: UGC

Ya yaba wa mata bisa gagarumar gudummawar da suke bayarwa wajen dorewar zamantakewar tattalin arzikin kasar, tun daga hanyoyin yanke shawara har zuwa yankunan karkara, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce, “Ina matukar alfahari da nasarorin da tsohuwar Ministar Muhalli ta samu kuma a yanzu mataimakiyar Sakatare Janar ta Majalisar Dinkin Duniya (UN), Amina Mohammed.

"Fatima Mohammed Kyari a matsayin Mai Kula ta dindindin ga Maajalisar Dinkin Duniya yankin Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) da kuma sabuwar zababbiyar Darakta (DG) na Kungiyar Kasuwanci ta Duniya (WTO), Dr Ngozi Okonjo-Iweala."

Shugaba Buhari ya ci gaba da cewa tagwayen sharri na rashin damar samun ilimi da talauci da cin zarafin jinsi sun kasance masu matukar hana mata shiga harkokin siyasa da shugabanci.

“Duk da haka, kudurinmu bai girgiza ba wajen magance wadannan matsalolin.

"Duk da irin abubuwan da suka faru na sace yara ‘yan makaranta da sauran kalubalen tsaro, wannan gwamnatin na nan daram a kokarin ta na ganin an samu al’umma mai adalci da gaskiya ba tare da nuna bambanci ba da kuma inganta doka.

"Ina mai tabbatar muku duka cewa mun dage da yin aiki tare da kungiyoyi irin naku don magance wadannan kalubalen.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun harbe hadimin Sanata Aliyu Wammako a Sokoto

A wani labarin daban, Shugaba Joe Biden na kasar Amurka ya yi tuntube sau uku kuma ya fadi kan matakalan jirgin Air Force One a ranar Juma'a, wanda ya haifar da alamar tambaya game da lafiyarsa, in ji jaridar The Telegraph.

Shugaban mai shekara 78 - wanda shi ne shugaban da ya fi tsufa a tarihin shugabannin Amurka - ya bayyana a wani bidiyo yana fama dakyar yayin hawa jirgin shugaban kasar.

Ya haura kusan kashi daya cikin uku na matakalan jirgin saman, kwasam ya yi tuntube, wanda tuni ya yi wuf ya kama karfen gefe daa gefen matakalan jirgin.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.