Yawan yaran da basa zuwa makaranta ya karu da miliyan 3 cikin watanni uku

Yawan yaran da basa zuwa makaranta ya karu da miliyan 3 cikin watanni uku

- Karamin ministan ilimi, Emeka Nwajiuba, ya ce yara miliyan 10 ne ke gararamba ba sa zuwa makaranta a Najeriya

- Ya ce idan Najeriya na son magance matsalar, toh wajibi ne sai ta inganta bangaren ilimi ta hanyar tunkarar matsalolin da ke hana yara halartar makaranta

- Sai dai kuma Nwajiuba bai bayyana abubuwan da suka haddasa karuwar yara marasa zuwa makarantu ba

Karamin Ministan Ilimi, Emeka Nwajiuba, ya bayyana adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar a yanzu zuwa miliyan 10.

Hakan na nufin an samu karin yara 3,054,000 da ba su halartar makarantu a cikin shekara guda da ta wuce.

Ministan Ilimi, Adamu Adamu, a farkon wannan watan na Janairu ya ce yawan yaran da ba sa zuwa makaranta wanda ya kai miliyan 10.1 a shekarar 2019 ya ragu zuwa miliyan 6.946 a shekarar 2020.

Yawan yaran da basa zuwa makaranta ya karu da miliyan 3 cikin watanni uku
Yawan yaran da basa zuwa makaranta ya karu da miliyan 3 cikin watanni uku Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kashe jami’an sojojin ruwa da na yan sanda 6 a Anambra

Amma a yayin bikin kaddamar da ingantacciyar cibiyar bayar da Ilimi ta Bai-daya ta Duniya (BEDSA) a Dutse, Jihar Jigawa, Nwajiuba ya ce: “Da kimanin yara 10,193,918 da ba su zuwa makaranta, Najeriya ce ke da mafi yawan wadanda ba sa zuwa makaranta a yankin Afirka ta kudu da Sahara. "

Nwajiuba bai ambaci abubuwan da ke haifar da karuwar wannan adadi ba, amma ta ce don Najeriya ta magance wadannan kalubalen yadda ya kamata, dole ne ta karfafa ingancin ilimin firamare ta hanyar tunkarar matsalolin da ke hana yara damar samun ilimin zamani.

Ministan ya ce jihar Jigawa na daga cikin jihohin da suka fi fama da wannan matsalar.

Ya ce kaddamar da shirin a Jigawa ya kasance nuna godiya ga kokarin da gwamnatin jihar ke yi na farfado da bangaren da ke fama da koma baya.

Ya ce baya ga Jagawa, wasu jihohi 16 da suka hada da Jihohin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas da kuma Neja, Ribas, Oyo da kuma Ebonyi, za su amfana da shirin.

Ya ce johohin za su ci gajiyar shirin ne gwargwadon adadin yaran a jihohin.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihohi da na tararayya da masu ruwa da tsaki su hada hannu wajen magance matsalolin da ke tarnaki ga cigaban kasar.

KU KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun far ma kasuwar Zamfara, sun kashe mutum daya tare da kona shaguna

Gwamnan Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar ya ce a yunkurin gwamnatinsa na magance matsalar, ta dauki malamai 1,393 aiki a 2018.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng