Rundunar yan sanda ta halaka 'yan fashi 2 a wani artabu da suka yi a Jihar Kaduna

Rundunar yan sanda ta halaka 'yan fashi 2 a wani artabu da suka yi a Jihar Kaduna

- Wasu yan bindiga biyu sun hadu da ajalinsu a hannun jami'an yan sandan jihar Kaduna

- Lamarin ya afku ne a karamar hukumar Lere da ke jihar a ranar Laraba

- An tattaro cewa maharan na shirin kaddamar da wani mummunan hari ne a garin Saminaka a lokacin da jami’an suka bude masu wuta

Jami’an 'yan sanda a Jihar Kaduna sun yi nasarar halaka 'yan fashi biyu ranar Laraba yayin wani artabu a karamar hukumar Lere da ke jihar.

An tattaro cewa 'Yan fashin na shirin kaddamar da wani mummunan hari ne a garin Saminaka a lokacin da jami’an hadin gwiwar suka far musu bayan samun wasu bayanan sirri.

KU KARANTA KUMA: Yawan yaran da basa zuwa makaranta ya karu da miliyan 3 cikin watanni uku

Rundunar yan sanda ta halaka 'yan fashi biyu a wani artabu da suka yi a Jihar Kaduna
Rundunar yan sanda ta halaka 'yan fashi biyu a wani artabu da suka yi a Jihar Kaduna Hoto: @PremiumTimesng
Asali: UGC

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige.

Jalige ya ce 'yan bindigar sun fara harbi bayan sun hangi jami'an tsaron, abin da ya haddasa zazzafar musayar wuta, sashin Hausa na BBC ya ruwaito.

Hakan ya sa 'yan sandan suka kashe biyu daga cikinsu sannan wasu suka tsere da raunuka sakamakon harbin bindiga.

KU KARANTA KUMA: Monguno: Babu Hadin Kan da ya Dace a Tsakanin Hukumomin Tsaron Kasar nan

Kakakin 'yan sandan ya kara da cewa sun kuma kwace makaman 'yan fashin da suka haɗa da bindigar AK-47 guda biyar da kwanson harsashi guda 17.

A wani labarin, mun ji cewa a kalla jami’an sojan ruwa uku da ‘yan sanda uku aka kashe a wurare daban-daban a fadin jihar ta Anambra.

Lamarin, wanda ya haifar da tashin hankali, ya kara rura wutar jita-jitar cewa wasu gungun 'yan daba sun mamaye jihar da nufin far ma jami'an tsaro.

An bayyana cewa yan ta’addan dauke da makamai sun kashe ‘yan sanda uku a mahadar Neni da ke karamar hukumar Anaocha na jihar, yayin da aka kona motarsu.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel