Yan bindiga sun kashe jami’an sojojin ruwa da na yan sanda 6 a Anambra

Yan bindiga sun kashe jami’an sojojin ruwa da na yan sanda 6 a Anambra

- Jami'an tsaro akalla shida ne suka hallaka a jihar Anambra

- Yan bindiga ne suka halaka jami'an tsaron wadanda suka hada da sojojin ruwa uku da yan sanda uku

- Ana rade radin cewa an sami wasu gungun 'yan bindiga da ke kai wa jami'an tsaro hari a jihar

Akalla jami’an sojan ruwa uku da ‘yan sanda uku aka kashe a wurare daban-daban a fadin jihar ta Anambra.

Lamarin, wanda ya haifar da tashin hankali, ya kara rura wutar jita-jitar cewa wasu gungun 'yan daba sun mamaye jihar da nufin far ma jami'an tsaro.

An bayyana cewa yan ta’addan dauke da makamai sun kashe ‘yan sanda uku a mahadar Neni da ke karamar hukumar Anaocha na jihar, yayin da aka kona motarsu.

Yan bindiga sun kashe jami’an sojojin ruwa da na yan sanda 6 a Anambra
Yan bindiga sun kashe jami’an sojojin ruwa da na yan sanda 6 a Anambra Hoto: newzandar.com
Asali: UGC

An kuma tattaro cewa an kashe jami’ai uku na Sojan Ruwa a Awkuzu, a Karamar Hukumar Oyi ta jihar.

KU KARANTA KUMA: NDLEA: Marwa yayi kira ga fara yiwa 'yan siyasa da dalibai gwajin shan kwayoyi

Wata majiya wacce ta nemi a sakaya sunan ta, ta ce ‘yan bindigar sun far wa jami’an ne a mahadar Awkuzu inda suka kashe uku daga cikin su nan take kafin su tafi da bindigogin su.

A cewar majiyar, jami’an sojan ruwa hudu suna bakin aiki a mahadar lokacin da ‘yan ta’addan suka afka musu da misalin karfe 2:00 na rana, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

“Dan Allah ku nemi wata hanyar idan kuna shirin tafiya zuwa wannan yankin. Dan Allah mu tsira da ranmu tukuna kafin yin tambayoyi a gaba. Irin wannan abu ya faru yan sa’o’i da suka wuce a mahadar Neni, gab da Oraukwum," kamar yadda yake a wani sako da aka yada a shafukan sada zumunta.

Jami'in hulda da jama'a na 'yan sanda a jihar ta Anambra, wanda ya fara aiki a ranar Laraba, DSP Tochukwu Ikenganyia, ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya ce ba shi da cikakken bayani.

Ya ce, "Ina tuntuba don samun cikakken bayani kafin in fitar da sanarwa kan lamarin kafin wani lokaci".

Wani babban jami'in 'yan sanda a rundunar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce "Abubuwan biyu sun faru amma ba zan iya tantance adadin wadanda suka rasa rayukansu ba a yanzu."

Anambra na cikin jihohin da aka kashe ‘yan sanda tare da kona ofisoshi a watan Fabrairu.

KU KARANTA KUMA: Monguno: Babu Hadin Kan da ya Dace a Tsakanin Hukumomin Tsaron Kasar nan

A wani labarin, rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce mutanenta sun kashe wasu 'yan bindiga biyu a Saminaka na karamar hukumar Lere ta jihar.

Rundunar ta kuma bayyana cewa abubuwan da aka kwato daga samamen sun hada da; bindigogin AK47 guda biyar, bindiga kirar G3 guda daya, tarin gidan alburusai guda 17 da kuma mota kirar Golf.

Kakakin rundunar, ASP Mohammed Jalige ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, yana mai cewa, wasu ‘yan bindiga da yawa sun tsere zuwa cikin daji sun bar makaman su na aikata barna.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel