Monguno: Babu Hadin Kan da ya Dace a Tsakanin Hukumomin Tsaron Kasar nan

Monguno: Babu Hadin Kan da ya Dace a Tsakanin Hukumomin Tsaron Kasar nan

- Mai bada shawara kan tsaron kasa, Babagana Monguno, yace babu hadin kai tsakanin hukomin tsaron kasar nan

- Monguno wanda yayi jawabi yayin taro da sakatarorin gwamnatin jihohi, ya ce dole ne a saka sarakunan gargajiya a harkar tsaro

- Babagana yace amfanin sarakunan gargajiya na da yawa ballantana wurin tattaro bayanan sirri a kan tsaro

Babagana Monguno, mai bada shawara kan tsaron kasa, yayi kira da hadin kai tsakanin hukumomin tsaro dake fadin kasar nan.

A yayin jawabi a ranar Alhamis a wani taron sakatarorin gwamnati a Abuja, NSA Monguno ya bukaci jihohi da su sauya salon karfafa tsarin tsaro a jihohinsu.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, ya kara da cewa akwai bukatar saka sarakunan gargajiya wurin tattaro bayanan sirri a jihohin kasar nan.

KU KARANTA: Sojin Najeriya sun sheke 'yan bindiga 2, sun cafke masu siyar da makamai a Kaduna

Monguno: Babu Hadin Kan da ya Dace a Tsakanin Hukumomin Tsaron Kasar nan
Monguno: Babu Hadin Kan da ya Dace a Tsakanin Hukumomin Tsaron Kasar nan. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bidiyon Garri, gyada, sikari da aka raba wurin kayataccen biki sun janyo cece-kuce

"Idan aka ki saka shugabannin al'umma, ba za a samu bayanan sirri da ake bukata ba," Monguno yace.

"A halin yanzu, hukumomin tsaro basu aiki tare kamar yadda ya dace. Muna ta kokarin ganin hadin kansu.

“Ko muna so, ko bama so, Najeriya ta dogara da masarautun gargajiya. Suna da matukar muhimmanci ga tsaro kuma idan suka dauka nauyin da ke kansu, ba za mu iya kwacewa ba saboda siyasa.

“Ba wai baiwa jama'a sarauta bane. Dole ne mu yi amfani dasu sannan suma su nuna kokarinsu."

Monguno yayi kira da sakatarorin gwamnatocin jihohi da su koma jihohinsu kuma su sasasanta da shugabanninsu domin gane amfanin sarakunan gargajiya.

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta damke wani matashi da yayi sanadin mutuwar wani dattijo mai shekaru 60 kuma mahaifin abokinsa bayan ya lakada masa mugun duka.

Kakakin rundunar 'yan sandan, DSP Abdullahi Kiyawa, ya tabbatar da aukuwar lamarin a yammacin Talata.

Lamarin ya faru ne a unguwar sheka dake birnin Kano sakamakon takaddamar da ta hada matashin da mahaifin abokinsa.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng