Matsalarmu ba shugabancin 2023 bane, adalci muke so a yiwa mutane, Makinde

Matsalarmu ba shugabancin 2023 bane, adalci muke so a yiwa mutane, Makinde

- Gwamnan jihar Oyo ya bukaci 'yan jiharsa da su mayar da hankali kan batun rashin tsaro

- Ya nemi da a bar maganar shugabancin kasa na 2023 a magance matsaloli da yiwa jama'a adalci

- Ya kuma bayyana cewa, ba kujerar gwamna bane ta dame shi, bai kuma damu ya fadi a zabe ba

Seyi Makinde, gwamnan Oyo, ya ce yankin kudu maso yamma ya kamata ya mai da hankali wajen ganin an yi adalci ga wadanda suka aikata laifuka ne, maimakon mayar da hankali zuwa zaben shugaban kasa na 2023, The Cable ta ruwaito.

Ya bayyana hakan ne a taron majalisar yarbawa da aka gudanar a ranar Laraba a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Makinde, wanda ya yi kira da a hada kai don magance matsalar rashin tsaro, ya ce a ko yaushe zai dauki shawarar da za ta amfani mutane.

KU KARANTA: Majalisar wakilai ta nemi Buhari ya yi hayar mayakan waje don yakar Boko Haram

“Kafin na zama gwamna, na tsaya takara har sau uku. Me zai tsorata ni? Me yasa ba zan yi daidai ba? Ina da kwarin gwiwar cewa bana tsoron wata wahala.

"Ba ni da ubangida na siyasa sai Allah. Allah ne ya kawo ni wannan mukami, don haka ba na tsoron kowa komai karfin mutumin nan,” in ji gwamnan.

“Na tsaya ne a kan mutuncina cewa zan yanke shawara domin amfanin jama’ata. Wasu mutane suna magana game da 2023.

"Wannan shugabancin ya kamata ya zo yankin yamma, amma ba batun yanzu ba ne. Batun da ya kamata mu fuskanta a yanzu shi ne yadda mutane za su sami adalci.

“Babu bukatar zubar da jini, ya kamata mu guje hakan. Hikima ta fi amfani da iko. Ya kamata mu tunkari batun da kyakkyawar hikima don guje wa asara.

"Kamar yadda nake tsaye a gabanku, idan ban sake zama gwamna ba, zan koma gida. Ban damu da matsayin ba, na damu ne game da ci gaban walwala da ci gaban jihar Oyo da kasar Yarbawa.”

Gwamnan ya kuma bayyana matakan da ya dauka don magance rashin tsaro a jihar, ya kara da cewa gwamnati za ta dauki jami'ai da ba 'yan jihar ba a kokarin sa na samar da aikin dan sandan cikin gida.

KU KARANTA: NAFDAC: Wata bakuwar cuta daga gubar abinci ta bullo a jihar Kano

A wani labarin daban, Wani rikici ta barke a majalisar dattawan Najeriya lokacin da 'yan majalisar ke tabka muhawara a kan wani kudurin da aka gabatar musu na bukatar a kafa hukumar da za ta kula da harkokin tsaron kasar, BBC Hausa ta ruwaito.

Wasu dai sun yi zargin cewa kudirin na nema ya kwace wa shugaban kasar ne ikonsa na nana hafsoshin tsaro.

Shugaban marasa rinjaye, Sanata Eyinnaya Abaribe ne ya gabatar da kudurin dokar, wanda wasu takwarorinsa daga bangarorin arewaci da kundancin kasar suka goya masa baya.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel