Rikicin Hijabi: Gwamnatin Kwara Ta Umarci Malaman Makaranta Su Koma Kan Aiki

Rikicin Hijabi: Gwamnatin Kwara Ta Umarci Malaman Makaranta Su Koma Kan Aiki

- Gwamnatin jihar Kwara ta umarci malaman makarantar da rikicin hijabi ya shafa da su koma bakin aiki

- Shugaban hukumar kula da malamai (TSB) na jihar Kwara, Bello Abubakar, ya bayyana cewa dukkanin shuwagabanni da Malaman makarantu 10 da abin ya shafa su koma aiki ranar 19 ga watan Maris.

- Gwamnatin ta rufe makarantun ne biyo bayan taƙaddamar da aka samu kan saka Hijabi a makarantar.

Shugaban hukumar dake kula da malaman sakandire (TSB) na jihar Kwara Bello Abubakar ya umarci daukacin shugabannin makarantu 10 da aka rufe tare da malamansu da su koma bakin aiki ranar 19 ga watan Maris shekarar 2021.

KARANTA ANAN: ‘Yan bindiga sun dura Kauye a Tegina, sun sace Fasto, sun ce sai an biya Naira Miliyan 60

A wani bayani da kakakin hukumar ilmi na jihar, Amogbonjaye Peter, ya fitar, yace ya zama wajibi malaman su koma domin ƙara horar da ɗaliban dake fuskantar jarabawar ƙarshe ta gama sakandire.

Rikicin Hijabi: Gwamnatin Kwara Ta Umarci Malaman Makaranta Su Koma Kan Aiki
Rikicin Hijabi: Gwamnatin Kwara Ta Umarci Malaman Makaranta Su Koma Kan Aiki Hoto: @Daily_trust
Asali: Twitter

Malam Bello yace duk wani malamin da ya kuskura bai koma ba, to lallai zai fusƙanci fushin hukumar ilmi ta jihar, domin kuwa su ba zasu lamunci rashin ɗa'a ba.

Sannan ya kirayi jama'a a kan su daina ɗaukar doka a hannun su inda ya kara jaddada cewa lallai ne a cigaba da yin zama tsakanin gwamnati da masu ruwa da tsaki don ganin cewa an samu daidaito.

Shugaban ya bayyana cewa gwamnati bata ji daɗin abinda ya faru ba da ya janyo har aka rufe makarantun, sai dai anyi hakan ne don amfanin ɗaliban, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Kashe $1.5bn don gyaran matatar man Fatakwal, da lauje cikin nadi: Cewar Atiku

Sannan ya kirayi iyayen yara da sauran al'umma akan su kwantar da hankulansu domin kuwa gwamnatin na ƙoƙarin magance matsalar.

An dai kulle makarantun guda 10 ne biyo bayan wasu ƙungiyoyin kiristoci da suke ƙoƙarin hana ɗalibai mata musulmai sanya hijabi a makarantun da suke iƙrarin cewa nasu ne.

A wani labarin kuma 'Yan bindiga sun harbe wani matashi, sun yi awon gaba da Uwa da Ɗanta a Jigawa

Wasu yan bindiga sun kai hari gidan wani mutum a garin Kawo, dake karamar hukumar Birnin Kudu, jihar Jigawa

Mutanen da ba'a san ko su waye ba sun harbi mutum ɗaya sun kuma yi awon gaba da mahaifiyarsa da ɗan uwansa.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262