'Yan bindiga sun harbe wani matashi, sun yi awon gaba da Uwa da Ɗanta a Jigawa
- Wasu yan bindiga sun kai hari gidan wani mutum a garin Kawo, dake karamar hukumar Birnin Kudu, jihar Jigawa
- Mutanen da ba'a san ko su waye ba sun harbi mutum ɗaya sun kuma yi awon gaba da mahaifiyarsa da ɗan uwansa
- Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, ta kuma ɗauki matakin gaggawa kamar yadda me magana da yawun ta ya faɗa
Wasu 'yan bindiga sun kashe wani matashi lokacin da suka kai hari a gidan mahifinsa a garin Kawo, Jihar Jigawa, yankin Arewa maso yammacin ƙasar nan.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Jihar ta Jigawa, Zahraddeen Aminuddeen, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Channels TV.
KARANTA ANAN: ‘Yan bindiga sun hallaka wani ‘Dan kasuwa a kauyen Katsina, sun yi gaba da ‘ya ‘yansa
Ya bayyana wanda lamarin ya faru akansa da suna Sabo Yusuf, ya ce an kai hari gidan mahifinsa da sanyin safiyar Laraba.
Aminuddeen ya ƙara da cewa yan bindigar sun harbi Yusuf a kirji inda akai gaggawar kaishi asibitin Birnin Kudu, amma aka tabbatar da rai ya yi halinsa.
A cewar Aminuddeen:
"Da misalin karfe 3:25 na safe, hukumar yan sanda ta sami labarin cewa wasu mutane da ba'a san ko suwa ye ba sun haura gidan wani Mutumi a garin Kawo, karamar hukumar Birnin Kudu, suka harbi ɗan sa a ƙirji ɗan kimanin shekara 25."
"'Yan bindigan sun yi awon gaba da matar mutumin da kuma ɗan uwan wanda aka kashe zuwa wani wuri da ba'a sani ba. An yi gaggawar kai matashin da aka harba babban Asibitin duba mara lafiya dake Birnin kudu amma likita ya tabbatar da rai ya yi halinsa." inji mai magana da yawun 'yan sanda.
KARANTA ANAN: Rikicin Hijabi: Ba zamu yarda da duk wani yunƙurin CAN ba, Inji MURIC
Ya kara da cewa, tuni kwamishinan 'yan sanda ya tura jami'an 'yan sanda masu yaƙi da sace-sacen mutane zuwa inda lamarin ya faru.
Ya ce an kuma ba jami'an umarnin kuɓutar da waɗan da aka kama, kuma su kamo waɗan da suka aikata wannan mummunan aikin don su fuskanci hukunci.
Jihar Jigawa ta kasance cikin kwanciyar hankali duk da tayi iyaka da jihar Kastina, da kuma jihar Yobe.
Sai dai a kwanan nan jihar na fuskantar satar mutane da kuma harin 'yan bindiga a wasu kauyaku na kananan hukumomin dake jihar.
Ranar 25 ga watan Disamban shekarar data gabata, wasu 'yan bindiga suka harbe jami'an tsaro biyu kuma suka jikkata a karamar hukumar Garki dake Jihar Jigawa.
A wani labarin kuma Cin Hanci Da Rashawa Ne Ya Raba Ku Da Mulki, APC Ta Maida Martani Ga PDP
Jam'iyya mai mulkin ƙasar nan APC ta maida zazzafan martani ga babbar jam'iyyar adawa PDP bayan caccakar da tasha daga wajen PDP ɗin a kwanakin baya
APC tace yawaitar cin hanci da rashawa yasa 'yan Najeriya suka juya ma PDP baya a zaben 2015.
Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.
Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.
Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77 .
Asali: Legit.ng