Dalilin da ya sa na kagi garkuwa da kaina, amaryar Kano

Dalilin da ya sa na kagi garkuwa da kaina, amaryar Kano

- Amaryar Kano da aka yi zargin an sace ta fito ta bayyana gaskiyar lamari

- Amina Gwani Danzarga ta ce ta kagi garkuwa da kanta ne saboda ta daina son angon nata

- Sai dai ta daura alhakin hakan a kan sharrin shaidan inda ta nemi afuwar iyayenta

Amina Gwani Danzarga, amaryar da ta boye awanni 48 kafin bikin aurenta, ta bayyana dalilin da ya sa ta dauki matakin.

Tun da farko ‘yan uwanta sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa an yi garkuwa da Amina ne a kan hanyarta ta dawowa daga unguwar Dorayi inda ta je ta ajiye katin jarrabawarta.

Amma daga baya sai‘yan sanda suka ba da sanarwar cewa amaryar ce da kanta ta shirya hakan.

Dalilin da ya sa na kagi garkuwa da kaina, amaryar Kano
Dalilin da ya sa na kagi garkuwa da kaina, amaryar Kano Hoto: Food.jumia.com.ng
Asali: UGC

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya shaida wa jaridar cewa budurwar ta buya ne saboda ba ta son a gudanar da bikin auren.

KU KARANTA KUMA: Alkali ya yi wa EFCC kashedi, ya ja wa Lauyanta kunne a shari’ar Shehu Sani

Amina ta amsa aikata laifin, inda ta bayyana cewa ta dauki wannan matakin ne saboda bata son saurayin nata.

"Ba na son saurayin, shi ya sa na dauki wannan hukuncin… Duk da cewa ni ce na nuna shi ga mahaifana," in ji ta.

Amina ta kara da cewa, kasancewar tana ganin girman iyayenta sosai, ba za ta iya sanar da su cewa ta sauya tunaninta game da mai neman ta ba.

Sai dai kuma, ta ce, a yanzu tana son mai shirin zama ango nata fiye da da kuma a shirye ta ke ta zauna da shi cikin lumana har tsawon rayuwarta.

Ta kuma nemi afuwar iyayenta da mijin da za ta aura, inda ta bayyana cewa sharrin shaidan ne ya kai ta ga aikata hakan.

Kawun Amina, Gwani Rayyanuna, ya nuna kaduwa game da juyawar lamarin.

“Har yanzu ina cikin kaduwa da abin da yarinyar ta aikata. Ita ce ta gabatar mana da shi kuma na yi bincike game da saurayin kuma a matsayinmu na iyaye, mun yi dukkan tsare-tsaren da suka dace game da bikin auren ”.

"Ba ta sanar da mu komai game da canjin ra’ayi da ta yi ba, sai yanzu da muka ji wani labarin na daban daga wurinta," in ji shi.

KU KARANTA KUMA: Matsalarmu ba shugabancin 2023 bane, adalci muke so a yiwa mutane, Makinde

Da aka tambaye shi kan yadda mataki na gaba zai kasance, Gwani Rayyanuna ya ce dangin za su hadu su yanke shawara.

Lokacin da aka tuntube shi, mai shirin zama angon nata, Umar Hassan, ya ki cewa komai kan batun, yana mai cewa har yanzu bai hadu da ita ba.

A baya mun ji cewa kwana biyar bayan an yi garkuwa da ita, har yanzu ba a san inda wata amarya da za a yi a Kano, Amina Gwani Danzarga take ba.

An tattaro cewa an sace Amina, wacce ke zaune a Unguwar Koki a cikin birnin Kano a ranar Juma'a, kwanaki biyu kafin bikinta.

Ganin karshe da ’yan uwa suka yi wa Amina wacce daliba ce a Kwalejin Tarayya da ke Kano, shi ne yayin da ta fita daga gida zuwa makaranta a yammacin ranar Juma’a.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng