Alkali ya yi wa EFCC kashedi, ya ja wa Lauyanta kunne a shari’ar Shehu Sani

Alkali ya yi wa EFCC kashedi, ya ja wa Lauyanta kunne a shari’ar Shehu Sani

- Hukumar EFCC ta koma kotu da tsohon Sanatan Kaduna, Shehu Sani

- Lauyan Shehu Sani ya kai wa Alkali karar bayanan da EFCC ta ke yi

- Alkalin kotu ya yi wa hukumar ta EFCC kashedi a kan jirkita bayanai

Inyang Ekwo, Alkali mai shari’a a babban kotun tarayya da ke garin Abuja, ya gargadi hukumar EFCC a wajen shari’ar da ake yi da Sanata Shehu Sani.

Jaridar Premium Times ta ce Alkali Inyang Ekwo ya gargadi EFCC ne a kan jirkitar da hujjoji a shari’ar da ake yi da tsohon Sanatan Kaduna, Shehu Sani.

Alkali mai shari’a ya yi wannan kashedi ne bayan da lauyan wanda ake zargi, Abdul Ibrahim SAN, ya koka kan wani bayani da EFCC ta yi a shafinta na Twitter.

Kara karanta wannan

APC ta Fallasa Abinda Ya Kawo Hargitsi A Gangamin PDP na Kaduna

Lauyan da ya tsaya wa Shehu Sani ya na zargin hukumar EFCC da amfani da shafinta na Twitter wajen canza bayanai a wannan shari’ar da ta ke gaban Alkali.

KU KARANTA: Ana zargin Okoi Obono-Obla da laifin satar N10m - ICPC

Inyang Ekwo ya ja hankalin hukumar da cewa ba mutanen gari su ke yanke wa wanda ake tuhuma hukunci ba, ya ce Alkali ne kadai mai zartar da hukunci a kotu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mai shari’a Ekwo yake cewa; “Tun da aka fara shari’ar nan, na fada cewa duk bayanan da ake nema su na nan a fili, kowa zai iya samunsu, har da ‘yan jarida.”

“Ba na so in sake jin labarin ana canza bayanai.” Ekwo ya gargadi EFCC da ta shigar da kara a kotu.

Da aka zauna a ranar Laraba, lauyan wanda ake kara ya duba shaidun EFCC da hujjojin da su ka bada.

Kara karanta wannan

Mai neman takarar Sanata da Gwamnan APC Ya Shiga Uku, An Rufe Shi a Gidan Yari

Alkali ya yi wa EFCC kashedi, ya ja wa Lauyanta kunne a shari’ar Shehu Sani
Sanata Shehu Sani Hoto: Legi.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Shehu Sani ya maka EFCC a kotu, ya bukaci a biya sa diyya

Bayan an saurari shaidu goma, Alkali ya ki ba EFCC dama ta kira wani shaidan, sannan ya ce dole Ekele Iheanacho ya cigaba da zama a matsayin lauyan hukumar

Alkalin ya dakatar da shari’ar, ya ce kotu za ta cigaba da zama a ranar 24 ga watan Mayu, 2021.

A makon nan ne EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta cigaba da shari’a da tsohon 'dan majalisar Kaduna, Shehu Sani, idan za ku tuna.

Bayan an zabi Alkalin da zai saurari wannan karar, an zauna an saurari hujjar da aka gabatar na wata wayar salula tsakanin Shehu Sani da Alhaji Sani Dauda.

EFCC ta na tuhumar Sani da laifuffuka biyu, daga ciki akwai karbar kudi daga hannun Attajirin.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Kara karanta wannan

2023: Da Ace Ni Ba Dan PDP Bane, Da Zan Taimaki Peter Obi Ya Zama Shugaban Kasa, Gwamnan Arewa

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng