Sojin Najeriya sun sheke 'yan bindiga 2, sun cafke masu siyar da makamai a Kaduna

Sojin Najeriya sun sheke 'yan bindiga 2, sun cafke masu siyar da makamai a Kaduna

- Sojojin rundunar Operarion Thunder Strike sun sheke 'yan bindiga biyu a Rafin Rikamba dake Chikun a Kaduna

- Dakarun sun kai samame ne har sansanin miyagun 'yan bindigan amma wasu daga cikin miyagun sun tsere

- An cafke wasu mutum biyu 'yan gida daya da ake zargin suna siyarwa 'yan bindiga makamai tun daga Bauchi

Dakarun Rundunar Operation Thunder Strike sun kashe 'yan bindiga biyu yayin da wasu suka arce da miyagun raunika a samamen da suka kai sansanin 'yan bindigan dake Rafin Rikamba dake karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

An tattaro cewa wani matukin babbar mota da 'yan bindigan suka sace ya samu tserewa a samamen.

Hakazalika, 'yan sanda sun damke wasu mutum biyu da ake zargi, Abdullahi Samaila da Adamsu Samaila daga karamar hukumar Toro ta jihar Bauchi dauke da harsasai na siyarwa da suka boye a murfin mota.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, wadanda ake zargin sun bayyana cewa su ke samar da makamai ga wasu Marcus Danladi, Danjuma Dachi da Ibrahim Haruna, da aka kama a watan Fabrairu.

KU KARANTA: Bidiyon Garri, gyada, sikari da aka raba wurin kayataccen biki sun janyo cece-kuce

Sojin Najeriya sun sheke 'yan bindiga 2, sun cafke masu siyar da makamai a Kaduna
Sojin Najeriya sun sheke 'yan bindiga 2, sun cafke masu siyar da makamai a Kaduna. Hoto daga @BBCHausa
Asali: UGC

KU KARANTA: Tsaka mai wuya: Kotu ta aika Wakili gidan yari a kan zargin kisan kai, garkuwa da mutane

Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan a wata takarda da ya fitar, yace su ukun an kama su da harsasai carbi 1,565 a ranar 28 ga watan Fabrairun.

Aruwan yace wadanda aka kama din sun yi kokarin tserewa amma Adamu Samaila ya samu miyagun raunika wadanda suka yi sanadiyyar mutuwarsa. Sai dai Abdullahi Samaila ya samu rauni a kafarsa ta dama.

Kamar yadda yace, wani Suleiman Tukur da dansa Shuaibu Sulaiman sun shiga hannun hukuma bayan an gane suna siyarwa da 'yan bindiga makamai.

A wani labari na daban, rundunar 'yan sanda a ranar Talata ta damke wata kungiyar masu laifi 9 dake siyar da bindigogi kala-kala ga 'yan bindigan daji, masu fashi da makami, masu garkuwa da mutane da sauransu.

Daga cikin wadanda ake zargin kuma aka kama, akwai wani mai suna Anthony Base, wanda aka kama, aka gurfanar sannan aka kai shi gidan yari saboda wannan laifin amma sai wani gwamnan arewa maso yamma yayi masa rangwame aka sako shi.

A yayin da aka kai wadanda ake zargin tsohuwar hedkwatar sashi na musamman dake yaki da fashi da makami a Abuja, kakakin rundunar, Frank Mba, ya koka da yadda makamai da miyagun kwayoyi ke yawo a kasar nan.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng