An kama tsohon dan gidan fursuna da aka yi wa rangwame yana siyar da miyagun makamai ga 'yan ta'adda
- Rundunar 'yan sandan Najeriya ta damke wata kungiyar masu safarar miyagun makamai
- Rundunar ta kama wani Anthony Base wanda aka yi wa rangwame daga gidan fursuna
- An gano cewa su ke samarwa 'yan bindiga makamai, kwayoyi da harsasai a jihohin arewa
Rundunar 'yan sanda a ranar Talata ta damke wata kungiyar masu laifi 9 dake siyar da bindigogi kala-kala ga 'yan bindigan daji, masu fashi da makami, masu garkuwa da mutane da sauransu.
Daga cikin wadanda ake zargin kuma aka kama, akwai wani mai suna Anthony Base, wanda aka kama, aka gurfanar sannan aka kai shi gidan yari saboda wannan laifin amma sai wani gwamnan arewa maso yamma yayi masa rangwame aka sako shi.
A yayin da aka kai wadanda ake zargin tsohuwar hedkwatar sashi na musamman dake yaki da fashi da makami a Abuja, kakakin rundunar, Frank Mba, ya koka da yadda makamai da miyagun kwayoyi ke yawo a kasar nan.
KU KARANTA: Hotunan shugaba Buhari yayin da ya karba bakuncin shugaban kasan Nijar a Aso Rock
KU KARANTA: Manyan motocin alfarmar da shugaban Miyetti Allah ke hawa sun janyo cece-kuce
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa, ya jaddada cewa jami'an FIB, STS da rundunar IGP ta IRT, karkasin umarnin CP Abba Kyari da DCP Kolo Yusuf ba za su tsagaita ba a farautar masu laifi.
Mba ya bayyana cewa, an samu miyagun makamai 10, harsasai 2,496, kwalayen Tramadol wadanda za su kai darajar miliyan 3, buhunan wiwi, naura mai kwakwalwa 2, wayoyi 8 da mota kirar Golf daya wacce ke kai da kawowa 'yan bindiga makamai.
A wani labari na daban, mayakan Boko Haram dauke da makamai sun shiga kauyen Katarko dake karamar hukumar Gujba ta jihar Yobe inda suka kone wata makarantar firamare da dakin shan magani.
Lamarin ya faru da karfe 5:30 na safiyar Talata yayin da Musulmai ke sallar Asubahi. Katarko gari ne mai nisan kilomita 18 daga Damaturu wanda ke fuskantar hare-hare masu tarin yawa har da tashin bam a wata gada da ta hada Katarko da Buni Yadi da Biu a baya.
Vanguard ta ruwaito cewa, wani mazaunin yankin mai suna Mohammed Ahmed ya tabbatar da cewa 'yan ta'addan sun fatattaki sojoji wanda hakan yasa jama'a suka dinga neman wurin tsira.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng