Tsaka mai wuya: Kotu ta aika Wakili gidan yari a kan zargin kisan kai, garkuwa da mutane

Tsaka mai wuya: Kotu ta aika Wakili gidan yari a kan zargin kisan kai, garkuwa da mutane

- Kotun majistare mai zama a Ibadan, babban birnin jihar Oyo ta aike da Iskilu Wakili gidan yari

- Kamar yadda kotun ta bayyana, ana zarginsa da kisan kai, garkuwa da mutane tare da fashi

- Iskilu Wakili ya shiga hannun 'yan sanda bayan jami'an OPC sun kama shi kuma ya musanta zargin da ake masa

Wata kotun majistare dake zama a Ibadan, jihar Oyo, ta bukaci a adana mata gagararren shugaban masu garkuwa da mutane, Iskilu Wakili, a gidan gyaran hali a kan zarginsa da ake yi na kashe mutane, hada kai wurin cuta, garkuwa da mutane da fashi da makami.

An gurfanar da wanda ake zargin tare da wasu a gaban kotu sakamakon laifuka shida da ake zarginsu dasu.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa an gurfanar da Wakili ne tare da Samaila, Aliyu Many da wani Abu mai shekaru 45 a duniya.

KU KARANTA: Hotunan shugaba Buhari yayin da ya karba bakuncin shugaban kasan Nijar a Aso Rock

Tsaka mai wuya: Kotu ta aika Wakili gidan yari a kan zargin kisan kai, garkuwa da mutane
Tsaka mai wuya: Kotu ta aika Wakili gidan yari a kan zargin kisan kai, garkuwa da mutane. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Manyan motocin alfarmar da shugaban Miyetti Allah ke hawa sun janyo cece-kuce

Lagit.ng ta ruwaito cewa wasu jami'an OPC ne suka kwamushe Iskilu Wakili wanda ake zargi da zama gagarumin mai garkuwa da mutane.

Sai dai tun bayan da aka kama Wakili, ya musanta dukkan zargin da ake masa a gaban 'yan sanda inda yace bai taba kisan kai ko garkuwa da mutane ba.

A wani labari na daban, Grand Croix Des Ordre National Du Niger, ita ce lambar yabo mafi daraja ta kasar Nijar kuma an baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, 16 Maris, 2021.

Wannan karramawar na daga cikin abubuwan da suka faru yayin da shugaban kasa Mahamadou Issoufou ya ziyarci shugaban kasa Buhari a fadarsa dake Abuja a ranar Talata.

Buhari yace shugaban abun koyi ne tare da taya shi murnar kammala mulkinsa karo na biyu da kuma nasarar kyautar Mo Ibrahim da ya samu ta shugabancin Afrika.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel