Bidiyon Garri, gyada, sikari da aka raba wurin kayataccen biki sun janyo cece-kuce

Bidiyon Garri, gyada, sikari da aka raba wurin kayataccen biki sun janyo cece-kuce

- Wata ma'abociyar amfani da kafar sada zumunta ta wallafa bidiyon wani irin abinci da ake rabawa wurin biki

- An ga masu raba abinci suna raba garri, gyada, kifi, kankara da sukari ga manyan bakin da suka halarta

- Jama'a a kafafen sada zumunta sun bayyana ra'ayoyinsu yayin da wasu ke kallon haka da cigaba

Wani dan Najeriya mai amfani da @uzomathias a Twitter ya janyo hankalin jama'a inda suka dinga maganganu bayan wani bidiyo da ya wallafa na biki ana bada abinci.

A bayyane, mai raba abincin a bikin ya nuna Garri, kifi, gyada, sikari da kankara a cikin kayan tagomashin da za a baiwa bakin da aka tara.

A wani bidiyo da @uzomathias ya wallafa, an ga mai bada abincin yana zuba garri a kwano inda yake hadawa da sikari, gyada da kankara a sama.

KU KARANTA: Tsaka mai wuya: Kotu ta aika Wakili gidan yari a kan zargin kisan kai, garkuwa da mutane

Hotunan Garri, gyada da kankara da aka raba wurin kayataccen biki sun janyo cece-kuce
Hotunan Garri, gyada da kankara da aka raba wurin kayataccen biki sun janyo cece-kuce. Hoto daga @uzomathias
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Jamhuriyar Nijar ta baiwa Buhari lambar yabo mafi daraja

A tiren, an ga katon kifi mai yaji. An ga mai raba abincin dauke da kwanukan garri shida, lamarin da ke nuna cewa baki da yawa na son wannan abun dadin.

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kaduna tace ba za ta rufe makarantu ba bayan tsanantar hare-haren 'yan bindiga a makarantu, yankuna da kuma sauran sassa na jihar.

Wannan na zuwa ne bayan ganawar da Gwamna Nasir El-Rufai yayi da sarakunan gargajiya, malaman addinai da sauran masu ruwa da tsaki a ranar Talata, inda mazauna jihar suka goyi bayan gwamnan a kan kada yayi sasanci da 'yan bindiga.

Channels Tv ta wallafa cewa, a yayin jawabi a taron, gwamnan ya jaddada cewa gwamnati za ta yi aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki a kan yadda zata shawo kan kalubalen tsaro da ke damun jihar Kaduna.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng