Gwamna Masari ya kalubalanci yadda Gumi yake wa 'yan bindiga, yana tafka kuskure

Gwamna Masari ya kalubalanci yadda Gumi yake wa 'yan bindiga, yana tafka kuskure

- Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya kalubalanci yadda Sheikh Gumi ya bullowa 'yan bindiga

- Gwamnan yace kamata yayi a farko Gumi yayi musu wa'azi kan illar, fyade, sata, fashi, garkuwa da mutane da sauransu

- Masari yace kwata-kwata salon Gumi ba zai kawo mafita ba ga rashin tsaron da ya addabi kasar nan ba

Aminu Masari, gwamnan jihar Katsina yace baya goyon bayan yadda Ahmad Gumi, fitaccen malamin addinin Islama ke zuwa domin sasantawa da 'yan bindiga.

Gumi yana kan gaba wurin jan hankalin gwamnati a kan ta sasanta da 'yan bindiga duk da yadda suka tsananta wurin kai hare-hare tare da satar 'yan makaranta.

The Cable ta ruwaito yadda Malamin ke kaiwa 'yan bindiga ziyara a inda suke buya cikin dajikan kasar nan domin kokarin kawo sasanci da kuma shawartarsu da su ajiye makamansu.

KU KARANTA: Bidiyon Garri, gyada, sikari da aka raba wurin kayataccen biki sun janyo cece-kuce

Gwamna Masari ya kalubalanci tattaunawar Gumi da 'yan bindiga, yace yayi kuskure
Gwamna Masari ya kalubalanci tattaunawar Gumi da 'yan bindiga, yace yayi kuskure. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Tsaka mai wuya: Kotu ta aika Wakili gidan yari a kan zargin kisan kai, garkuwa da mutane

A yayin tsokaci a kan salon Gumi, gwamnan jihar Katsina yace ba yadda ya dace a shawo kan lamarin Gumi yake yi ba.

"'Yan bindiga na bukatar karatun addini da kuma dabi'a tagari domin su san muhimmancin rayuwar jama'a kuma su daina kisa da fyade," Masari ya sanar a ranar Laraba yayin zantawa da gidan talabijin na Channels.

“Bana goyon bayan Gumi saboda baya yin abun yadda ya dace. Na yi tsammanin da farko zai yi musu wa'azi a kan illar kashe jama'a, garkuwa dasu, fyade, sata da sauransu.

"Abinda muke tsammanin malamin addini zai fara musu kenan."

A wani labari na daban, rahotanni dake zuwa daga jihar Zamfara dake arewa maso yammacin kasar nan na nuna cewa miyagun 'yan bindiga sun halaka mutum takwas, ciki har da sojoji uku bayan wata arangama da suka yi.

Hakazalika, wasu mutum bakwai da suka matukar jigata suna asibiti inda suke samun taimakon likitoci sakamakon hari da 'yan bindigan suka kai a kauyen a ranar Talata.

Mummunan labarin na zuwa ne bayan sa'o'i kadan da 'yan bindiga suka kaiwa Sarkin Birnin-Gwari, Alhaji Zubairu Idris Maigwari II hari.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel