'Yan bindiga sun sheke sojojin Najeriya 3 a jihar Zamfara

'Yan bindiga sun sheke sojojin Najeriya 3 a jihar Zamfara

- Miyagun 'yan bindigan daji sun sheke sojojin Najeriya 3 a jihar Zamfara

- Sojojin da 'yan bindigan dajin sun yi arangama inda farar hula 5 da soji 3 suka ce ga garinku

- Kamar yadda aka gano, wasu mutum bakwai na kwance a gadon asibiti bayan arangamar

Rahotanni dake zuwa daga jihar Zamfara dake arewa maso yammacin kasar nan na nuna cewa miyagun 'yan bindiga sun halaka mutum takwas, ciki har da sojoji uku bayan wata arangama da suka yi.

Hakazalika, wasu mutum bakwai da suka matukar jigata suna asibiti inda suke samun taimakon likitoci sakamakon hari da 'yan bindigan suka kai a kauyen a ranar Talata.

Mummunan labarin na zuwa ne bayan sa'o'i kadan da 'yan bindiga suka kaiwa Sarkin Birnin-Gwari, Alhaji Zubairu Idris Maigwari II hari.

KU KARANTA: An kama tsohon dan gidan fursuna da aka yi wa rangwame yana siyar da miyagun makamai ga 'yan ta'adda

'Yan bindiga sun sheke sojojin Najeriya 3 a jihar Zamfara
'Yan bindiga sun sheke sojojin Najeriya 3 a jihar Zamfara. Hoto daga @BBCHausa
Asali: UGC

KU KARANTA: Hotunan shugaba Buhari yayin da ya karba bakuncin shugaban kasan Nijar a Aso Rock

'Yan bindiga na cigaba da cin karensu babu babbaka a yankin arewa maso yammacin kasar nan inda suke kai miyagun hare-hare har da makarantu.

A wani labari na daban, mayakan Boko Haram dauke da makamai sun shiga kauyen Katarko dake karamar hukumar Gujba ta jihar Yobe inda suka kone wata makarantar firamare da dakin shan magani.

Lamarin ya faru da karfe 5:30 na safiyar Talata yayin da Musulmai ke sallar Asubahi. Katarko gari ne mai nisan kilomita 18 daga Damaturu wanda ke fuskantar hare-hare masu tarin yawa har da tashin bam a wata gada da ta hada Katarko da Buni Yadi da Biu a baya.

Vanguard ta ruwaito cewa, wani mazaunin yankin mai suna Mohammed Ahmed ya tabbatar da cewa 'yan ta'addan sun fatattaki sojoji wanda hakan yasa jama'a suka dinga neman wurin tsira.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng