Rundunar sojin Nigeria ta ragargaji mayakan Boko Haram a wani arangama
- Rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar kashe wasu mayakan Boko Haram a yankin Dikwa a jihar Borno
- Dakarun sojin sun samu wannan nasara ne tare da hadin gwiwar 'yan sintiri a yammacin ranar Litinin
- Sun kuma yi nasarar kwato motoci biyu da bindigogin kirar AK 47 da saurar wasu nau'ukan makamai masu hadari
Sojojin Najeriya na ci gaba da samun nasara a harin da suke kai wa 'yan ta'addan Boko Haram, ISWAP da sauran su.
Dakarun Bataliya ta 81 tare da hadin gwiwar' yan kato da gora a yammacin ranar Litinin, 15 ga Maris, sun kashe karin 'yan ta'addan a yankin Dikwa, Jihar Borno.
A wani artabu da sojoji suka yi karkashin atisayen "TURA TAKAIBANGO, sun fatattaki mayakan Boko Haram da dama a yankin Dikwa - Ajiri a karamar hukumar Dikwa da ke jihar.
KU KARANTA KUMA: Buhari, AGF Malami sun jaddada cewa IGP Adamu zai iya zama a kujerarsa har 2024
Sojojin da ke sintiri sun hade da 'yan ta'addar da ke kan babura da motar bindiga, cikin hanzari suka yi musayar wuta da su, inda suka kashe mutum shida daga cikinsu sannan kuma suka kwato makamai da dama, da alburusai da kayayyakin amfanin gona.
Kayayyakin da aka kama a yayin artabun sun hada da PKM 1, bindigogin AK 47 guda biyu, da sauran wasu nau'ukan makamai masu hadari.
Sauran kayayyakin sun hada da babura guda 2, mujalla guda 1, wayoyin hannu guda biyu da kuma bututu.
Hakazalika, sojojin kamfanin Bravo yayin da suke gudanar da makamancin wannan aikin zagayen a ranar 15 ga watan Maris, sun gano wata wayar salula.
Ana zargin 'yan ta'addan da suka gudu ne suka bar salular yayinda dakarun soji suka bude masu wuta a lokacin da suke kokarin kutsawa sansanin a ranar 14 ga Maris , 2021.
An mika wayar hannun ga rundunar leken asiri na soji domin bincikenta.
KU KARANTA KUMA: Shugaban EFCC ya samu damar yin gwanjon dukiyoyi da kadarorin babban Soja
Daraktan hulda na jama’a na rundunar soji, Birgediya Janar Mohammed Yerima, ya bayyana cewa kamar yadda yake a umarnin Babban hafsan sojan kasa, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru, sojoji za su ci gaba da jajircewa don tabbatar da ganin cewa an tsarkake yankin baki daya.
Hakazalika ya ce za su kare yankin inda suka mamaye duk wata hanyar da ake zargin 'yan ta'adda suna zirga-zirga domin fitar da su.
A wani labarin, mun ji cewa hukumomin bataliya ta bakwai ta gidan sojojin kasa, ta yarda ta dawo da sojojin bataliya ta 153 da ke garin Marte, jihar Borno.
Jaridar Daily Trust ta ce an dawo da sojojin bakin-aiki ne bayana an karbe khakinsu da takardar aiki bayan ‘yan Boko Haram sun kai masu wasu hare-hare.
‘Yan ta’addan Boko Haram sun samu galaba a kan jami’an sojojin kasar a wasu hare-hare da aka kai a cikin watannin Junairu da Fabrairun wannan shekarar.
Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.
Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.
Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.
Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411
Asali: Legit.ng