PDP: Gwamnatin APC yaudarar 'yan Najeriya kawai take, ba wani aiki da take samarwa

PDP: Gwamnatin APC yaudarar 'yan Najeriya kawai take, ba wani aiki da take samarwa

- Jam'iyyar PDP ta zargi gwamnatin shugaba Buhari da dabi'ar yaudarar 'yan Najeriya

- PDP tace gwamnatin Buhari na yaudarar 'yan Najeriya ne da cewa tana samar da ayyuka

- A cewar PDP, rashin iya mulki ne ya jawo gwamnatin APC ke yaudarar 'yan Najeriya da samar da ayyuka

Jam’iyyar adawa ta PDP ta zargi jam’iyyar APC da take jagorancin Gwamnatin Tarayya da yiwa ‘yan Najeriya karya kan aikin yi da samar da ayyukan yi.

Ta yi wannan zargin ne a cikin wata sanarwa a ranar Talata daga Sakataren ta na Yada Labarai na Kasa, Kola Ologbondiyan, dangane da rahoton da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar kan yawaitar marasa aikin yi a kasar.

Gidan Talabijin na Channels ya bayar da rahoton cewa 33.3% da aka samu a zango na hudu na shekarar 2020 ya karu da 6.2% bisa dari sama da 27.1% bisa dari da aka samu a zango na biyu a shekarar da ta gabata.

Babbar jam'iyyar adawar ta yi imanin cewa sabon adadi na rashin aikin yi tabbaci ne kai tsaye cewa ikirarin samar da dimbin ayyukan yi da gwamnatin ke kumfan baki akai karya ce kawai da ake amfani da ita wajen yaudarar mutane.

KU KARANTA: Abdurrasheed Bawa ya bukaci ma'aikatan banki da su gaggauta bayyana kadarorinsu

PDP: Gwamnatin APC yaudarar 'yan Najeriya kawai take, ba wani aiki da take samarwa
PDP: Gwamnatin APC yaudarar 'yan Najeriya kawai take, ba wani aiki da take samarwa Hoto: The Guardian Nigeria
Asali: UGC

Ta yi zargin cewa rahoton da NBS ya bayar, na cewa miliyoyin 'yan Najeriya masu karfin hali sun rasa ayyukansu da kuma hanyoyin samun abin yi yayin da yawa kuma suka zama marasa aikin yi, ya nuna halin kunci da gwamnatin ta jefa al'ummar kasar.

“Hauhawar rashin aikin yi daga 27.1% bisa ɗari a cikin zango na 2, 2020 zuwa 33.3% cikin dari a cikin zango na huɗu na shekarar 2020, duk da ikirarin da gwamnatin APC ke yi na karya, ya tabbatar da cewa hakika, babu wani fatan ci gaba a gaban Shugabancin Buhari da APC.

“A bayyane yake cewa babban abin da ke haifar da karuwar rashin aikin yi shi ne rashin iya mulki da yaduwar almundahana da dukiyar kasa a cikin gwamnatin Buhari."

Jam'iyyar ta PDP ta kuma zargi shugabannin APC da yin sama da fadi da dukiyar al'umma.

Jam'iyyar ta yi tir da halin da rashin aikin yi a tsakanin matasa daga shekaru 15 zuwa 34 da ya haura zuwa 42.5%.

Jam’iyyar adawar ta ce a bayyane take cewa Gwamnatin Tarayya ta kirkiro da ayyukan yi ne kawai a cikin bayanan kididdigarta na bogi yayin da a zahiri, ba ta daukar wasu kwararan matakai don karfafawa ‘yan kasa masu kwazo.

KU KARANTA: Dalilan da suka sanya jihar Kano haramta sayar da lemon dan tsami

A wani labarin, Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Sojoji, Sanata Ali Ndume, ya ce zai saba wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC ace arewa ta samar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar na gaba, Daily Trust ta ruwaito.

Dan majalisar, wanda ke wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattijai, ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da kungiyar Correspondents' Chapel, kungiyar 'yan jaridu ta Najeriya da Majalisar Tarayya ta shirya a ranar Asabar.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel