Hukumar JAMB Ta Tuhumi Ma'aikatanta biyu Kan Badaƙalar Gurbin Shiga Jami'a
- Hukumar JAMB ta kama wasu ma'aikatan ta guda biyu da laifin amsar kuɗaɗe a hannun iyayen yara da zummar samar musu guraben karatu
- Waɗanda ake tuhuma ɗin sun amsa laifin su na amsar cin hanci a hannun wasu iyayen yara 4
- Shugaban JAMB yace basani ba sabo akan duk wanda aka kama da cin hanci a hukumar ko waye shi.
A ranar Litinin ɗin nan, hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu (JAMB) ta tuhumi wasu ma'aikatanta guda 2 da laifin karbar kuɗaɗe hannun wasu ɗalibai da zummar sama musu gurbin karatu a makarantun gaba da sakandire.
Daya daga cikin waɗanda ake tuhuma wanda ma'aikaci ne mai mataki na 12 a ofishin hukumar reshen jihar Delta, ya amsa cewa lallai ya karɓi kuɗi N500,000.
KARANTA ANAN: Madalla! Malamin da aka sace a jami'ar Patakwal ya kuɓuta
Yace ya amshi kuɗaɗen ne a hannun iyayen yara 4 inda kuma daga ciki ya bawa abokin aikin shi mai mataki na 8 ,N180,000 wanda shima ya kasance ma'aikaci ne a hukumar.
Ɗaya daga cikin iyayen yaran ne ya aike da ƙorafi zuwa ga ofishin hukumar dangane da badaƙalar da ma'aikatan keyi wanda daga nan ne hukumar ta shiga bincike kan lamarin.
Babban wanda ake tuhumar ya shaida ma manema labarai cewa yanayin da Najeriya ke ciki na matsin tattalin arziƙi ne ya sanya shi shiga cikin wannan badaƙala.
Sai dai ɗayan me laifin (mai mataki na 8) ya bayyana cewa harkar kiwon kifi ce ta haɗasu da babban me laifin.
Daga baya kuma ya bayyana cewa akwai yiwuwar asirce shi yayi, domin shi bai san ta yadda akayi ya shiga wannan shirgi ba.
"Abun ba hakan nan ba, saboda ni ban ma sanshi ba, iyaka dai kawai ya kirana a waya da haka ne ya jani zuwa wannan cuwa-cuwa. Sannan ya faɗa min cewa ai shi ya daɗe a irin wannan harkar." a cewar ƙaramin ma'aikacin.
KARANTA ANAN: Da duminsa: Shugaban majalisa, Ahmad Lawan, ya yi allurar rigakafin Korona, za'a yiwa sauran Sanatoci
Shugaban hukumar JAMB ta ƙasa, Farfesa Ishaq Oloyede, yace ya kaɗu matuƙa da ganin cewa a cikin ma'aikatan hukumarsa aka samu wannan mummunar al'ada ta cin hanci duk da yadda yake yaƙi da hakan.
Shugaban ya sha alwashin cewa za'a hukunta ko wanene aka samu da aikata irin hakan.
"Ko wanene aka samu da aikata irin wannan laifuka na cin hanci, to lallai babu wata kariya da hukumar zata bashi domin hukumar bata goyon bayan cin hanci ta kowace fuska." inji shugaban JAMB.
Oloyede ya shawarci iyayen yara akan su daina yarda suna bama wasu kuɗi da zummar wai zasu samar ma 'ya 'yansu guraben karatu.
Domin kuwa yanzu an zamanantar da tsarin ta yadda babu wani abu da wani zai iya akan hakan. Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
A wani labari kuma Ministan Buhari ya bayyana yadda tsohon Shugaban hukumar EFCC, Magu zai kare.
Ministan shari’ar ya ce dokar kasa za ta yi aiki a wajen binciken Magu da ake yi.
Malami ya ki bada amsa ko gwamnati za ta shiga kotu da tsohon shugaban EFCC.
Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.
Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.
Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77.
Asali: Legit.ng