Buhari, AGF Malami sun jaddada cewa IGP Adamu zai iya zama a kujerarsa har 2024

Buhari, AGF Malami sun jaddada cewa IGP Adamu zai iya zama a kujerarsa har 2024

- Rikita-rikitar dake tattare da kara wa'adin mulkin IGP Mohammed Adamu a halin yanzu tana gaban kotu

- Daga shugaban kasa Muhammadu Buhari har ministan shari'a na Najeriya, AGF Malami, sun kare abinda suka yi

- Lauyoyin Buhari da na Malami sun ce karin wa'adin mulkin shugaban 'yan sandan dama ce da Buhari yake da ita

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Antoni janar na tarayya, Abubakar Malami sun ce kundin tsarin mulkin kasar nan ya baiwa shugaban kasa Buhari damar rike IGP Mohammed Adamu a kujerarsa iyakar son ransa.

Matsayarsu tana kunshe ne a wani martanin hadin guiwa da suka fitar sakamakon kalubalantarsu da Lauya Maxwell Opara yayi a kan karin wa'adin mulkin Adamu a lokacin da ya dace a ce yayi murabus.

KU KARANTA: Hare-haren 'yan bindiga: Ba za mu garkame makarantun jihar Kaduna ba, El-Rufai

Buhari, AGF Malami sun jaddada cewa IGP Adamu zai iya zama a kujerarsa har 2024
Buhari, AGF Malami sun jaddada cewa IGP Adamu zai iya zama a kujerarsa har 2024. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Jamhuriyar Nijar ta baiwa Buhari lambar yabo mafi daraja

A takardar da lauya Maimuna Shiru ta fitar a madadin Buhari da Malami, ta ce Adamu dan sanda ne mai aiki kuma zai iya mora daga karin wa'adin mulkinsa daga shugaban kasa Buhari.

Lauyan ta bayyana cewa, shekaru hudu na wa'adin mulkin IGP dake sashi na 7, sakin layi na 6 na dokokin ayyukan 'yan sanda na 2020, zai kare ne a 2023 ko 2024.

Kamar yadda tace: "Idan aka kirga wa'adin mulkinsa daga 2020, lokacin da sabuwar dokar ayyukan 'yan sandan ta fara aiki, wa'adin mulkinsa zai kare ne a 2024."

A wani labari na daban, a makon nan ne majalisar koli ta addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) ta bayyana nisabin karancin sadaki a kasar nan.

Jaridar Legit.ng ta samu zantawa da Sheikh Khamis Al-Misriy, limamin masallacin Abu Ubaidah Bn Jarrah dake bye-pass jihar Kaduna domin samun karin haske.

Kamar yadda malamin ya sanar, nisabi dai shine wani ma'auni da ake gwadawa domin a gane darajar kudi da inda ya kai. A musulunce kuwa ana kiran shi da kaso daya bisa hudu na dinari daya.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel