Hare-haren 'yan bindiga: Ba za mu garkame makarantun jihar Kaduna ba, El-Rufai

Hare-haren 'yan bindiga: Ba za mu garkame makarantun jihar Kaduna ba, El-Rufai

- Malam Nasir El-Rufai yace jihar Kaduna ba za ta rufe makarantu ba a kan harin 'yan bindiga

- Ya sanar da hakan ne a wani taro da yayi da sarakunan gargajiya tare da masu ruwa da tsaki na jihar

- Gwamnan yace ana cigaba da nema tare da kokarin ceton 'yan makarantar da aka sace a Mando Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna tace ba za ta rufe makarantu ba bayan tsanantar hare-haren 'yan bindiga a makarantu, yankuna da kuma sauran sassa na jihar.

Wannan na zuwa ne bayan ganawar da Gwamna Nasir El-Rufai yayi da sarakunan gargajiya, malaman addinai da sauran masu ruwa da tsaki a ranar Talata, inda mazauna jihar suka goyi bayan gwamnan a kan kada yayi sasanci da 'yan bindiga.

Channels Tv ta wallafa cewa, a yayin jawabi a taron, gwamnan ya jaddada cewa gwamnati za ta yi aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki a kan yadda zata shawo kan kalubalen tsaro da ke damun jihar Kaduna.

KU KARANTA: Mayakan Boko Haram sun yi wa makiyaya 22 kisan gilla a garin Monguno dake Borno

Hare-haren Kaduna: Makarantu zasu kasance a bude, El-Rufai
Hare-haren Kaduna: Makarantu zasu kasance a bude, El-Rufai. Hoto daga Channeltv.com
Asali: UGC

Taron da aka yi shi bayan kwanaki biyar da 'yan bindiga suka sace dalibai 39 na kwalejin horar da aikin noma dake Afaka a karamar hukumar Igabi ta jihar.

Yayin da ake cigaba da neman daliban, Gwamna El-Rufai yace an duba yanayin tsaron jihar kuma gwamnati ta yanke hukuncin cewa ba za ta rufe makarantu ba.

El-Rufai yace gwamnatin na cigaba da neman maganin kalubalen tsaro na jihar kuma aikinsa a matsayinsa na gwamna shine tabbatar da doka tare da taimakawa wurin hukunta masu laifi.

KU KARANTA: Kyakyawar budurwa da kawayenta 5 sun zama likitoci, hotonsu ya gigita jama'a

A wani labari na daban, 'yan Najeriya sun yi caa a kan wasu hotunan shugaban Miyetti Allah Kautal Hore da suka watsu a kafafen sada zumuntar zamani inda ya bayyana a wasu motocin alfarma da kuma 'yan sanda na yi masa rakiya.

Duk da ba a san inda shugaban kungiyar ya nufa ba, amma hotunan sun nuna cewa a cikin gari yake tare da tawagarsa mai dauke da motoci uku kirar SUV tare da wasu adaidaita sahu da 'yan sanda ke tsaron lafiyarsa.

Wasu 'yan Najerya sun kwatanta shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore da rayuwar alfarma wacce take a bayyane amma makiyaya na wata rayuwa ta daban.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng