Kyakyawar budurwa da kawayenta 5 sun zama likitoci, hotonsu ya gigita jama'a
- Kyakyawar budurwa tare da kawayenta biyar sun samu nasarar kammala karatunsu na zama cikakkun likitoci
- Mutane da yawa da suka ga hoton kawayen a shafin Twitter sun jinjinawa irin wannan kawance da nasara
- Akwai wadanda suka dinga tambayar asibitin da kyawawan 'yammatan za su dinga aiki don su dinga kai ziyara
Masu hikima na cewa tsintsiya madauri daya ta fi shara da kyau, tsinke daya ba zai iya ba. Sau da yawa idan aka hada kai an fi cimma nasarar abinda ake nema fiye da mutum daya ya tsaya shi kadai.
Wata matashiyar budurwa mai amfani da @dr_kay_umar ta tabbatar da wannan zancen ga duniya bayan ta wallafa hotonta da kawayenta.
A ranar Asabar, 13 ga watan Maris ne ta wallafa hotonta da kawayenta wadanda dukkansu sun zama likitoci a rana daya.
KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Mahaifin Ngozi Okonjo-Nweala, Farfesa Okonjo, ya rasu
KU KARANTA: Yari ga Matawalle: Kayi taka-tsan-tsan da yadda kake kula da tsaron jihar Zamfara
Dukkansu sun bayyana sanye da rigar likitoci inda suke dauke da murmushi. Mutane da yawa sun dinga kwarzanta nasararsu inda suke musu fatan alheri.
Ga wallafar da tayi:
Hoton ya dinga yawo a kafafen sada zumunta inda jama'a suka dinga tsokaci. Ga kadan daga cikin tsokacin jama'a:
@higherutley cewa yayi: "Wannan kawance haka, Ina muku fatan samun duk abinda kuke so a aikinku. Babu mata da yawa a ajinmu a lokacin da nake makarantar koyon likitanci."
@majidsyed30 tace: "MashaAllah, Allah yayi muku albarka da danginku kuma ya baku farin cikin da kuke fatan samu a duniya da lahira."
A wani labari na daban, dariqar Tijjaniya ta musanta baiwa tsohon sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II shugabancinta na Najeriya.
Sheikh Mahi Nyass, shugaban darikar Tijjaniya na duniya wanda ake kira da Khalifatum Arrm, ya bayyana hakan yayin da yayi jawabi ga manema labarai a Sokoto.
Jaridar The Punch ta wallafa cewa, Nyass, wanda shine da kuma magajin Shehu Ibrahim Nyass, yace in har za a yi nadi ana tantancewa sannan a zaba daga cikin mabiyanta na Najeriya da Senegal.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng