Manyan motocin alfarmar da shugaban Miyetti Allah ke hawa sun janyo cece-kuce

Manyan motocin alfarmar da shugaban Miyetti Allah ke hawa sun janyo cece-kuce

- Hotunan tawagar motocin da shugaban kungiyar Miyettei Allah ke yawo dasu sun janyo cece-kuce

- Kamar yadda aka gani, shugaban kungiyar na yawo da motocin alfarma tare da 'yan sanda dake tsaron lafiyarsa

- Lamarin yasa wasu 'yan Najeriya suka dinga caccakarsa domin ganin halin da makiyaya ke ciki amma shi yana morewa

'Yan Najeriya sun yi caa a kan wasu hotunan shugaban Miyetti Allah Kautal Hore da suka watsu a kafafen sada zumuntar zamani inda ya bayyana a wasu motocin alfarma da kuma 'yan sanda na yi masa rakiya.

Duk da ba a san inda shugaban kungiyar ya nufa ba, amma hotunan sun nuna cewa a cikin gari yake tare da tawagarsa mai dauke da motoci uku kirar SUV tare da wasu adaidaita sahu da 'yan sanda ke tsaron lafiyarsa.

Wasu 'yan Najerya sun kwatanta shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore da rayuwar alfarma wacce take a bayyane amma makiyaya na wata rayuwa ta daban.

KU KARANTA: Buhari ya sallami darakta janar na hukumar NiMet, yayi muhimman nade-nade 3

Dankareriyar motar alfarmar da shugaban Miyetti Allah ke hawa ta janyo cece-kuce
Dankareriyar motar alfarmar da shugaban Miyetti Allah ke hawa ta janyo cece-kuce. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

@EjioforOnyishi a Twitter cewa yayi, "Wannnan na iya yuwuwa ne kadai a mulkin Buhari, abun takaici."

@Isi_Miyake5 tace, "Sune masu fadi a ji a kasar nan. Me kuke tsammani? Babban yayansu yana fadar shugaban kasa."

Dankareriyar motar alfarmar da shugaban Miyetti Allah ke hawa ta janyo cece-kuce
Dankareriyar motar alfarmar da shugaban Miyetti Allah ke hawa ta janyo cece-kuce. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

@akunnenonso cewa yayi, "Duba dai 'yan sandan dake masa rakiya. Kai, gandun dabbobi."

Amma kuma wasu 'yan Najeriyan sun bayyana cewa wannan ba komai bane.

Misali @larucheebam cewa yayi, "Amma ai tsagerun Neja Delta na yawo da 'yan sanda a yankin kudu, don haka wannan ba matsala bace."

KU KARANTA: Mayakan Boko Haram sun yi wa makiyaya 22 kisan gilla a garin Monguno dake Borno

A wani labari na daban, Abdulaziz Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara, ya ja kunnen Bello Matawalle a kan siyasantar da kalubalen tsaro da ke addabar jihar.

A yayin jawabi ga manema Labarai a ranar Litinin a Talatan Mafara, Yari ya shawarci Matawalle da "yayi tunani mai zurfi a kan kowacce shawara da aka bashi wurin shawo kan matsalar tsaro."

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, ya bukaci Matawalle da ya hada kai da gwamnatin tarayya wurin shawo kan matsalar.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel