Gwamnatin Tarayya ta sanya ranar bude filin jirgin saman Kano
- Gwamnatin tarayya na shirin bude bangaren sufurin kasa da kasa na filin jirgin saman Mallam Aminu Kano
- Hadi Sirika, ministan sufurin jirage ya ce jiragen kasa da kasar za su fara jigila a filin jirgin saman Kano daga ranar 5 ga watan Afrilu
- Ya kuma ce za a sake bude filayen jiragen sama na Fatakwal da Enugu a ranar 15 ga Afrilu, 2021 da 3 ga watan Mayu, 2021
Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, a ranar Litinin ya ce za a sake bude filin jirgin sama na Malam Aminu Kano don jigilar jiragen kasa da kasa a ranar 5 ga Afrilun 2021.
Ya bayyana hakan ne a Abuja a yayin zaman kwamitin fadar Shugaban kasa kan annobar korona, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Ya kuma ce za a sake bude filayen jiragen sama na Fatakwal da Enugu don zirga-zirgar jiragen kasa da kasa a ranar 15 ga Afrilu, 2021 da 3 ga watan Mayu, 2021.
KU KARANTA KUMA: Hankali ya tashi: An sace amarya ana saura awanni 48 a daura auren ta
"An rufe filayen jirgin ne kamar yadda aka rufe na ko ina a duniya. Mun rufe filayen jirgin saman mu ne saboda ta nan ne wannan cuta ta shigo kasarmu.
"Mun bude wasu daga ciki, bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki. Babu wani dalili na kai da kai da ya hana a sake bude filin jiragen na Kano da sauran jihohi. Akwai matakan da ake bi," in ji Sirika.
Gwamnatin Tarayya, a farkon dokar hana zirga-zirga zuwa kasashen waje da na cikin gida, ta rufe filayen jiragen sama a Najeriya don hana shigowa da cutar.
Daga baya gwamnatin ta sake bude filayen sauka da tashin jiragen sama na Legas da Abuja domin zirga-zirgar kasashen duniya.
KU KARANTA KUMA: Hawaye sun kwaranya yayin da Atiku yayi babban rashi na hadiminsa watanni 2 bayan mutuwar matarsa
A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kano ta haramta sayar da sinadarin dan tsami da danginsa a fadin jihar baki daya, biyo bayan wata cuta da ake zargin sinadarin ya haifar ga jama'a.
Shugaban hukumar kare hakkin masu sayan kayayyaki Baffa Babba Dan Agundi ne ya bayyana hakan a hirar da ya yi da BBC.
Baffa ya ce bincike ya nuna cewa wadannan sinadaran da ake hada kayan shaye-shaye da su da yawansu lokacin ingancinsu ya kare, don haka babu mamaki dan an ce suna cutar da masu amfani da su.
Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.
Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.
Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.
Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411
Asali: Legit.ng