Ka cancanta: Buhari ya samu babbar lambar yabo mafi ƙololuwa a jamhuriyar Niger
- Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou ya ba shugaba Buhari na Najeriya lambar yabo mafi girma ta Nijar
- Ana kiran lambar yabon da aka bai wa Buhari da Grand Croix Des Ordre National Du Niger
- An ba shugaban Najeriyar lambar yabon ne saboda dangantaka da kishin ƙasa da kuma manufarsa ta ciyar da Afrika gaba
A ranar Talata ne aka baiwa Shugaban kasa Muhammadu Buhari lambar yabo mafi girma ta Jamhuriyar Nijar, wanda ake kira daGrand Croix Des Ordre National Du Niger.
Shugaban kasar Nijar mai barin gado, Mahamadou Issoufou ne ya karrama shi da lambar yabon.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da yada labarai, Femi Adesina ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa mai taken "Shugaba Buhari ya karbi lambar yabo mafi girma ta Jamhuriyar Nijar, yana taya shugaban mai barin gado Mahamadou Issoufou murna kan kyautar da ya samu ta Mo Ibrahim."
KU KARANTA KUMA: Abun farin ciki: Dalibar Kano da aka sace ana saura awanni 48 aurenta ta kuɓuta
Adesina ya nakalto shugaban yana taya Issoufou murnar kammala wa’adinsa na biyu cikin nasara, da kuma lashe babbar lambar yabo ta Mo Ibrahim ta nasarar da ya samu a shugabancin Afrika, yana mai bayyana shi a matsayin shugaban Afirka da ya cancanta.
Ya ce Buhari ya taya shugaban mai barin gado murna kan kiyaye ka'idojin dimokiradiyya, inganta tattalin arzikin kasarsa da kuma karfafa kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.
An ambato Buhari yana cewa “Ya Shugaban kasa, bari na fara da taya ka murnar kammala wa’adin ka na biyu a matsayin shugaban kasar ‘yar uwar mu, Jamhuriyar Nijar.
“Ina kuma taya mutanen kirki na Nijar murnar nasarar gudanar da zabe na gaskiya da adalci.
“Nasarorin da aka samu a lokacin da kake shugaban kasa sun samu karbuwa sosai ta hanyar lambar yabo ta Mo Ibrahim da ka samu kwanan nan.
KU KARANTA KUMA: An bayyana dalilin da yasa yan bindiga ke sace dalibai a arewa
"Ka samu kima da kaunar mutanen ka a gida da kuma 'yan uwan ka da ke iyakar Najeriya."
Buhari ya ce ziyarar sa ta farko bayan rantsar da shi a 2015 zuwa Jamhuriyar Nijar, yana mai cewa zabar kasa da ke makwabta ta nuna muhimmanci da ingancin alakar da ke tsakanin kasashen biyu.
A wani labari, Miss Sa'adat Aliyu da ta kirkiro wata manhaja da za ta ba wadanda aka yi wa fyade damar kai kara ba tare da tsangwama ba ta samu lambar yabo.
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Ibrahim Pantami FNCS, FBCS, FIIM ya karrama Sa’adat Aliyu a madadin gwammatin tarayya.
Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya mika wa wannan Baiwar Allah takardar yabo saboda kokari na fasahar da ta yi kamar yadda aka sanar a shafin Twitter.
Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.
Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.
Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.
Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411
Asali: Legit.ng