Abun farin ciki: Dalibar Kano da aka sace ana saura awanni 48 aurenta ta kuɓuta

Abun farin ciki: Dalibar Kano da aka sace ana saura awanni 48 aurenta ta kuɓuta

- An tsinci wata mai shirin zama amarya da aka yi garkuwa da ita a jihar Kano

- An tattaro cewa budurwar mai suna mina Gwani Danzarga bata ce uffan ba tun bayan bayyanarta saboda bata iya magana

- Zuwa yanzu dai danginta sun ce ba maganar daurin auren har sai ta dawo hayyacinta

An gano Amina Gwani Danzarga, wata mai shirin zama amarya a Kano, wacce aka tattaro cewa ta bata wasu ‘yan sa’o’i zuwa kafin aurenta.

Kawun Amina, Gwani Yahuza Gwani Danzarga, ya tabbatar da cewa an tsinci ‘yar dan uwan ​​nasa ne da safiyar Talata lokacin da dangin suka samu labarin cewa an ga wata yarinya a sansanin dalibai na jami’ar Bayero.

KU KARANTA KUMA: 2023: Rashin tabbas yayin da Atiku ke fuskantar yiwuwar hana shi takarar neman kujerar shugaban kasa

Abun farin ciki: Dalibar Kano da aka sace ana saura awanni 48 aurenta ta kuɓuta
Abun farin ciki: Dalibar Kano da aka sace ana saura awanni 48 aurenta ta kuɓuta Hoto: Admobi blog
Asali: UGC

“Wani ya kira mahaifiyar Amina ya gaya mata cewa an gano yarinyar a kan hanyar BUK. Da sauri muka je can muka tarar da Amina tana kuka”, in ji shi.

Ya kara da cewa tunda aka same ta, ba ta magana sai dai kawai tana magana da hannunta, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

"Muna godiya ga Allah da ya sada ta da dangin ta", in ji shi.

Da aka tambaye su yaushe ne za a yi auren, sai majiya daga dangin suka ce a yanzu haka an dakatar da auren har sai lokacin da yarinyar ta warke.

KU KARANTA KUMA: Hawaye sun kwaranya yayin da Atiku yayi babban rashi na hadiminsa watanni 2 bayan mutuwar matarsa

Da farko mun ji cewa kwana biyar bayan an yi garkuwa da ita, har yanzu ba a san inda wata amarya da za a yi a Kano, Amina Gwani Danzarga take ba.

An tattaro cewa an sace Amina, wacce ke zaune a Unguwar Koki a cikin birnin Kano a ranar Juma'a, kwanaki biyu kafin bikinta.

Ganin karshe da ’yan uwa suka yi wa Amina wacce daliba ce a Kwalejin Tarayya da ke Kano, shi ne yayin da ta fita daga gida zuwa makaranta a yammacin ranar Juma’a.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng