An bayyana dalilin da yasa yan bindiga ke sace dalibai a arewa

An bayyana dalilin da yasa yan bindiga ke sace dalibai a arewa

- Dakta Ahmed Adamu ya ce yan bindiga na satar dalibai ne saboda zakuwarsu na son tattaunawa da gwamnati

- Masanin harkokin shugabancin na jami'ar Nile, ya ce mahara na ganin cewa za su fi cin riba idan suka hadu kai tsaye da gwamnati fiye da garkuwa da daddaikun mutane

- Ahmed ya ce harin da ake kai wa makarantu ya jefa kasar cikin tsaka mai wuya tare da illata harkar ilimi a Arewacin Najeriya

Wani masanin harkokin shugabanci, Dakta Ahmed Adamu ya ce dalilin da ya sa yan bindiga ke yawan kai hare-hare a makarantu da sace dalibai shi ne cewa yan ta’addan sun zaku da son tattaunawa da gwamnati.

Ya ce: Yan bindigar na ganin idan gwamnati ta kasance dumu-dumu a cikin lamarin, za su fi samun riba.

“Sun ga abin da ya faru a baya lokacin da aka sace‘ yan matan Chibok kuma hakan ya ja hankalin duniya. Idan suna son irin wannan kulawar, sun san dole ne su karkata ga makarantu, ta hanyar satar dalibai, za su yi hulda da gwamnati kai tsaye,” Dakta Ahmed, wani malami a jami’ar Nile ya shaida wa jaridar Daily Trust.

An bayyana dalilin da yasa yan bindiga ke sace dalibai a arewa
An bayyana dalilin da yasa yan bindiga ke sace dalibai a arewa Hoto: @Vanguardngrnews
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: Hankali ya tashi: An sace amarya ana saura awanni 48 a daura auren ta

Ya ce 'yan bindigar sun fahimci cewa ta hanyar satar mutane, suna mu'amala da mutane ne kuma gwamnati ba za ta kula da hakan ba yana mai cewa, "galibi, mutanen da aka sace suna biyan kudin fansarsu kuma wadannan masu aikata laifin suna son yin suna, suna son kulawa."

Ya yi bayanin cewa raunin tsaro a makarantu ya sa suke samun saukin kutsawa su yi garkuwa da mutane masu yawa a lokaci daya, sannan su yi amfani da daliban a matsayin kariya daga harin rundunar sojoji.

“Wannan ne ya sa suke barazanar cewa idan har aka far musu da hari to za su kashe mutanen da ke hannunsu.

“Ka ga idan mutanen da ke hannun nasu na da yawa, to da wuya a kai musu hari saboda gwamnati ba za ta so a yi asarar rayuka da yawa ba,” inji shi.

Dakta Ahmed ya ce harin da ake kai wa makarantu ya jefa kasar cikin tsaka mai wuya tare da illata harkar ilimi a Arewacin Najeriya; Mutane da dama ba za su tura ’ya’yansu makaranta ba, sannan za a rufe makarantu da yawa.

KU KARANTA KUMA: Hawaye sun kwaranya yayin da Atiku yayi babban rashi na hadiminsa watanni 2 bayan mutuwar matarsa

“Wannan zai haifar da babban gibi tsakanin‘ ya’yan talakawa da ‘ya‘ yan attajirai kuma hakan zai haifar da karin wariya, rashin daidaito kuma hakan zai haifar da karin talauci.

"Hakan ya rage sha’awar tura yara makaranta a Arewa, kuma duk abin da ya illata ilimi na kawo koma-bayan cigaba da arziki da tsaron kasa, saboda yiwuwar marasa ilimi na shiga aikata miyagun laifuka,” inji shi.

A wani labarin, rundunar ‘yan sanda ta Zamfara ta sake sauya jami’inta na 'yan sanda (DPO) da ke Kaura-Namoda, sakamakon zargin da ake yi masa da hada baki da ‘yan bindiga da ke addabar yankin.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Mohammed Shehu, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka bayar ga manema labarai, a Gusau a ranar Litinin.

Ya kuma bayyana cewa, Kwamishinan 'yan sanda, Mista Abutu Yaro ya sauyawa DPO na yankin wurin aiki zuwa hedikwatar 'yan sanda a matsayin OC Provost, yayin da aka nada ASP Umar Abdullahi a matsayin DPO na yankin.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit

Online view pixel