Hawaye sun kwaranya yayin da Atiku yayi babban rashi na hadiminsa watanni 2 bayan mutuwar matarsa

Hawaye sun kwaranya yayin da Atiku yayi babban rashi na hadiminsa watanni 2 bayan mutuwar matarsa

- Louis Okoroma, hadimin tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku ya mutu

- Okoroma ya mutu a ranar Alhamis, 11 ga watan Maris, a cewar wata sanarwa da Ofishin yada labarai na Atiku ya saki

- Hadimin labaran ya mutu watanni biyu bayan mutuwar matarsa

Wani hadimin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, Louis Okoroma, ya mutu.

Mista Okoroma ya mutu a ranar Alhamis, watanni biyu bayan mutuwar matarsa, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Shugaban ofishin yada labaran Atiku, Paul Ibe, ya bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Litinin cewa marigayin ya kasance a wajen aiki a ranar Laraba kuma “ya yi mana bankwana lokacin da zai tafi ranar, amma ba mu san cewa wannan ne haduwarmu ta karshe da shi ba.”

Hawaye sun kwaranya yayin da Atiku yayi babban rashi na hadiminsa watanni 2 bayan mutuwar matarsa
Hawaye sun kwaranya yayin da Atiku yayi babban rashi na hadiminsa watanni 2 bayan mutuwar matarsa Hoto: Louis Okoroma
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: FG tayi martani ga ikirarin Asari Dokubo na kafa sabuwar gwamnatin Biafra

Mista Ibe ya bayyana Mista Okoroma a matsayin mutum mai faran-faran da jama’a kuma kwararren dan jarida wanda ya yi aikinsa cikin kwazo da jajircewa.

Ya kara da cewa Mista Abubakar da dukkanin ma'aikatan kungiyar "suna mika ta'aziyarmu ga danginsa, ciki har da 'ya'yansa."

Wani bangare na sanarwar ya ce:

“Mutuwar Mista Okoroma ta zo mana cikin firgita kuma za a ji mutuwar sa na tsawon watanni da shekaru masu zuwa saboda ba za a iya lissafa irin gudummawar da ya ba ofishinmu ba.

"Okoroma ba mutum mai faran-faran bane kawai, ya kuma kasance kwararren dan jarida wanda ya yi aikinsa cikin kwazo da jajircewa", cewar Mista Ibe.

KU KARANTA KUMA: 'Yan fashi sun far wa kwastoman banki da nufin kwace kudi N10m

A wani labarin, mun ji cewa za a iya hana tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar tsayawa takarar shugaban kasa idan har karar da ke neman a hana shi tayi nasara a kotu.

Sai dai dan siyasar ya nemi babbar kotun tarayya ta Abuja da ta yi watsi da karar wacce ke neman hana shi tsayawa takarar shugaban kasa a nan gaba.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa shari’ar da ke kalubalantar cancantar Atiku na tsayawa takarar shugaban kasa wata kungiya ce ta shigar da ita a karkashin inuwar Incorporated Trustees of Egalitarian Mission for Africa.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel