‘Yan sanda sun sake canza DPO a Zamfara bisa zargin hada baki da 'yan bindiga

‘Yan sanda sun sake canza DPO a Zamfara bisa zargin hada baki da 'yan bindiga

- Rundunar 'yan sanda a jihar Zamfara ta yi sauyin DPO a wani yankin jihar Zamfara

- Al'ummomin wani yanki a Zamfara na zargin DPO din da hada hannu da 'yan bindiga

Rundunar ‘yan sanda ta Zamfara ta sake sauya jami’inta na 'yan sanda (DPO) da ke Kaura-Namoda, sakamakon zargin da ake yi masa da hada baki da ‘yan bindiga da ke addabar yankin.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Mohammed Shehu, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka bayar ga manema labarai, a Gusau a ranar Litinin.

Shehu ya ce, "an ja hankalin rundunar 'yan sanda ta jihar Zamfara zuwa wani bidiyo mai yaduwa a shafukan sada zumunta inda al'ummomin kauyen Kungurki, a karamar hukumar Kaura Namoda, suka zargi DPO na Kaura Namoda da hada baki da wasu 'yan bindiga.

“Bayanan da aka samu a rundunar ba su bayyana wani korafi a kan jami'in ba game da zargin.

KU KARANTA: 'Yan fashi sun far wa kwastoman banki da nufin kwace kudi N10m

‘Yan sanda sun sake canza DPO a Zamfara bisa zargin hada baki da 'yan bindiga
‘Yan sanda sun sake canza DPO a Zamfara bisa zargin hada baki da 'yan bindiga Hoto: Channels Tv
Asali: UGC

“Amma, rundunar tana umartar jama’a, musamman al’ummar da suka fusata, cewa duk wani mutum ko wata kungiya da ke da kwararan shaidu a kan jami'in, ya zo Hedikwatar 'Yan sanda ya taimaka a binciken da ake yi.

"DPO, a matsayin mai kula da zaman lafiya da kwanciyar hankali, yana da ikon yin hulda tare da yin mu'amala da al'ummomin biyu na Hausawa da Fulani 'yan bindiga da ke fada da juna don tattaunawa da karfafa ayyukan ci gaban zaman lafiyar da gwamnatin jihar ke yi.

Ya kuma bayyana cewa, Kwamishinan 'yan sanda, Mista Abutu Yaro ya sauyawa DPO na yankin wurin aiki zuwa hedikwatar 'yan sanda a matsayin OC Provost, yayin da aka nada ASP Umar Abdullahi a matsayin DPO na yankin.

Shehu ya yi kira ga jama’a masu kwararan hujjoji kan tsohon DPO din da su tuntubi mai rikon matsayin na DPO din ta lambar wayarsa, 08162793939.

KU KARANTA: Ku kula da yaranku, ba zamu iya tabbatar da tsaro a duk makarantu ba, gwamnati ga iyaye

A wani labarin, Akalla mafarauta 17 aka kashe yayin da wasu 25 aka sace su, yayin harin wasu ‘yan bindiga da ke barna a dajin Tsayau da ke karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina.

Daya daga cikin mafarautan wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Litinin.

"Mun tabbatar da cewa an kashe 17… wasu daga cikin mutanen da suka je neman 'yan uwansu sun shaida mana cewa sun ga gawawwaki 17," in ji shi.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel